Gwamnan jihar Sokoto yayi umarnin biyan ma’aikata albashi saboda Azumi
Gwamnan jihar Sokoto Ahmed Aliyu ya bayar da umarnin biyan ma’aikatan jihar albashin watan Fabarairu nan take, saboda ƙaratowar watan azumin Ramadana.
Gwmnan ya sanar da hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fito ta hannun shugaban sashen yada labarai da hulɗa da jama’a na ofishin gwamnan, Abubakar Bawa a yau Alhamis.
Sanarwar ta ce matakin ya shafi: “ma’aikatan Gwamnatin jiha, ƙananan hukumomi, ma’aikatan hukumar Ilimi ta ƙananan hukumomi, da kuma tsofaffin ma’aikata masu karɓar fansho a faɗin jihar”.
Bayanin ya ƙara da cewa matakin fara biyan albashin zai fara aiki ne daga ranar Juma’a 13 ga watan na Fabarairu.
A ranar 18 ko 19 ga watan Fabarairun nan ne ake sa ran al’ummar Musulumi na duniya za su fara azumin watan Ramadana.