Gwamnatin Kano Ta Kaddamar da Sashen Kafofin Watsa Labarai na Zamani
Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da sabon Sashen Kafofin Watsa Labarai na Zamani (Digital Multimedia Department) a ƙarƙashin Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, domin ƙarfafa sadarwar gwamnati, inganta gaskiya da riƙon amana, tare da ƙara kusanci da al’umma ta hanyar amfani da fasahohin zamani.
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na jihar, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana hakan a yayin bikin ƙaddamar da sashen da kuma rantsar da dandalin daraktocin wayar da kai da hulɗa da jama’a, wanda aka gudanar a ranar Litinin a hedikwatar ma’aikatar da ke Sakatariyar Audu Bako, Kano.
Kwamared Waiya ya bayyana cewa kafa wannan sashe wani muhimmin gyara ne na hukumomi da aka yi domin magance gibin sadarwa tsakanin gwamnati da jama’a a wannan zamani na fasahar sadarwa.
Ya ce an samar da sabon sashen ne bayan gudanar da shawarwari da nazarin hukumomi, waɗanda suka nuna akwai buƙatar kafa wani tsari na musamman da zai riƙa tattara bayanan ayyukan gwamnati, nuna nasarorin da aka samu, yaɗa manufofi da kuma yaƙi da yaɗuwar labaran ƙarya ta hanyar samar da sahihan bayanai cikin gaggawa.
A cewarsa, sashen zai zama cibiyar samar da bayanai da shirya abubuwan da za a wallafa, hulɗa da jama’a ta yanar gizo, adana tarihin ayyukan gwamnati, wallafa bayanai da kuma gudanar da harkokin yaɗa labarai cikin tsari da ƙwarewa.
Kwamishinan ya yabawa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa amincewa da kafa sashen, yana mai cewa hakan ya nuna jajircewar gwamnati wajen inganta shugabanci mai amsa buƙatun jama’a da sadarwa mai inganci a ƙarƙashin manufar Kano First Agenda.
A wajen taron, an kuma ƙaddamar da Dandalin Daraktocin Wayar da Kai da Jami’an Hulɗa da Jama’a daga ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnati (MDAs) na jihar.
Ya ce an kafa dandalin ne domin ƙarfafa haɗin kai, musayar bayanai, haɓaka ƙwarewa da kuma samar da daidaito a tsakanin jami’an sadarwa na gwamnati.
A matsayin gudunmawa ga sabon dandalin, Kwamared Waiya ya sanar da bayar da gudunmawar Naira miliyan ɗaya (₦1,000,000) domin tallafa wa ayyukansa.
A saƙonnin fatan alheri da suka gabatar, Farfesa Nura Ibrahim, Farfesa Hassan Alhaji Ya’u, Dr. Saminu Umar Rigiyar Zaki na Sashen Sadarwa na Jami’ar Bayero Kano, Shugaban Dandalin Shugabannin Kafafen Yaɗa Labarai, Ado Sa’idu Warawa, Mataimakin Shugaban Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ), Mustapha Gambo, da Shugaban Dandalin Daraktocin Wayar da Kai da Hulɗa da Jama’a, sun yabawa kwamishinan da gwamnatin jihar bisa kafa sabon sashen, suna mai cewa hakan zai inganta tsarin sadarwar zamani na jihar tare da ƙarfafa isar da sahihan bayanai ga jama’a.
Sa hannu:
Sani Abba Yola
Daraktan Ayyuka na Musamman
Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida ta Jihar Kano
15 ga Yuni, 2026.