Mazauna Wuro Dole Na Tantance Asarar da sukayi Bayan Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Gidaje Da Gonaki A jahar Gombe

Mazauna garin Wuro Dole da ke Masarautar Gona a Karamar Hukumar Akko ta Jihar Gombe na ci gaba da kirga asarar da suka yi bayan wata mummunar ambaliyar ruwa da ta lalata gidaje, gonaki da sauran kadarori masu muhimmanci.

 

 

 

 

Ambaliyar ruwan ta biyo bayan ruwan sama mai karfi da aka yi a yankin, wanda ya tilasta wa iyalai da dama barin gidajensu tare da jefa su cikin halin kunci.

 

 

 

A yayin wata ziyara da ya kai yankin domin duba barnar da aka yi, shugaban rikon kwarya na Karamar Hukumar Akko, Abdullahi Abdulkadir, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici tare da jajanta wa al’ummar yankin bisa asarar da suka yi.

 

 

 

 

Abdulkadir, wanda ya jagoranci tawagar jami’an karamar hukumar da suka hada da Lamaran Ahmed da Muhammad Abubakar Ajiya, ya ce manufar ziyarar ita ce tantance girman barnar da kuma nuna goyon baya ga wadanda abin ya shafa.

 

 

 

 

Ya tabbatar wa mazauna yankin cewa gwamnati na sane da halin da suke ciki kuma za ta dauki matakan da suka dace domin tallafa musu.

 

 

 

yace  “Mun zo ne domin jajanta wa iyalan da abin ya shafa tare da tabbatar musu da cewa gwamnati ta san halin da suke ciki. Za mu tantance asarar da aka yi sannan mu yi duk mai yiwuwa wajen taimaka wa wadanda abin ya shafa,” in ji shi.

 

 

 

 

 

Ya kara da cewa jami’an sashen jin dadin al’umma za su gudanar da cikakken bincike kan gidajen da abin ya shafa domin saukaka rabon kayan tallafi da sauran nau’o’in taimako.

 

 

 

 

A nasa bangaren, Hakimin Wuro Dole, Hussaini Ishiyaku, ya yaba wa tawagar karamar hukumar bisa ziyarar da suka kai yankin, tare da yin kira ga hukumomin gwamnati, kungiyoyin agaji da sauran masu hannu da shuni da su tallafa wa wadanda ambaliyar ta shafa.

 

 

 

 

 

Ya kuma yi alkawarin gabatar da lamarin a zauren majalisar dokokin jihar domin jawo karin tallafi da shiga tsakani daga gwamnati.

 

 

Daya daga cikin wadanda ambaliyar ta shafa, Ali Zarami Bakin Boda, ya danganta aukuwar lamarin da ruwan sama mai karfi da kuma toshewar wata magudanar ruwa (culvert), lamarin da ya sa ruwa ya mamaye gidaje da gonaki.

 

 

 

Shi ma wani mazaunin yankin, Usman Munkaila, ya bayyana ambaliyar a matsayin babbar masifa da ta bar iyalai da dama ba tare da matsuguni ba.

 

 

 

 

 

 

Mazauna yankin sun bukaci a gaggauta daukar matakan tallafi domin su sake gina gidajensu, dawo da hanyoyin samun abin rayuwa da kuma farfadowa daga wannan mummunar ambaliyar ruwa.

 

You might also like
Leave a comment