Hukumar NSCDC Ta Dakile wani Yunkurin Garkuwa da Mutane da Satar Shanu a Kano
Hukumar Tsaro da Kare Kadarorin Al’umma ta Najeriya (NSCDC) reshen Jihar Kano ta ce jami’anta sun dakile wani yunkurin garkuwa da mutane da kuma satar shanu a Karamar Hukumar Kiru da ke jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, SC Ibrahim Idris Abdullahi, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis a Kano.
A cewarsa, lamarin ya faru ne a yankin Bakin Komau da ke karamar hukumar Dangora a Kiru, inda wasu mahara dauke da makamai suka kai hari kan wani makiyayi, suka yi masa munanan raunuka tare da yin garkuwa da ’ya’yansa biyu yayin da suke kokarin sace dabbobinsa.
Abdullahi ya ce jami’an NSCDC da ke bakin aiki a kusa da dajin Dansoshiya sun yi gaggawar kai dauki bayan samun kiran neman agaji, inda suka yi musayar wuta da maharan.
Ya bayyana cewa maharan sun yi watsi da wadanda suka yi garkuwa da su tare da tserewa zuwa cikin daji bayan sun kasa jure wa karfin farmakin jami’an tsaron, kuma ana zargin wasu daga cikinsu sun samu raunukan harbin bindiga.
yace “Gaggawar daukin da jami’anmu suka kai ya sa aka ceto wadanda aka yi garkuwa da su tare da hana satar shanun da maharan suka shirya,” in ji shi.
Mai magana da yawun rundunar ya bayyana sunayen wadanda aka ceto da Abubakar Saleh mai shekaru 36 da kuma Muhammadu Inuwa Dille mai shekaru 30, yana mai cewa tuni aka hada su da iyalansu.
Ya kuma ce makiyayin da ya samu raunuka, Alhaji Saleh mai shekaru 70, ya samu kulawar likitoci cikin gaggawa bayan harin.
Abdullahi ya kara da cewa an tura jami’an NSCDC yankin ne domin samar da tsaro ga aikin gina madatsar ruwa da ke gudana a wurin, tare da kare wuraren kiwo da al’ummomin manoma daga ayyukan miyagu.
A nasa bangaren, Kwamandan NSCDC na Jihar Kano, Mohammed Hassan Agalama, ya sake jaddada kudurin rundunar na kare rayuka, dukiyoyi da muhimman kadarorin kasa a fadin jihar.
Rundunar ta kuma bukaci mazauna yankunan da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai domin saukaka daukar matakan gaggawa kan barazanar tsaro da ayyukan ta’addanci.