Shugabannin Fulani Sun Yaba da Matakin Gwamnatin Kano Na Kwato Filayen Kiwo Da Aka Mamaye
Shugabannin Fulani sun yaba wa Gwamnatin Jihar Kano bisa kokarin da take yi na kwato filayen kiwo 371 da aka mamaye, hanyoyin dabbobi (Burtali/Labi) da sauran muhimman albarkatun makiyaya a fadin jihar.
Shugabannin kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN) da kuma kungiyar ci gaban Fulani ta Najeriya (FULDAN) ne suka bayyana hakan a tattaunawa daban-daban da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a ranar Asabar a Kano.
Shugaban MACBAN na Jihar Kano, Kyaftin Abdullahi Bakoji (mai ritaya), da takwaransa na FULDAN, Sani Adamu, sun bayyana cewa matakin da gwamnatin jihar ta dauka abin a yaba ne kuma hanya ce mai kyau ta kare filayen kiwo da hanyoyin dabbobi domin tabbatar da zaman lafiya tsakanin makiyaya da manoma.
Bakoji ya ce mamaye filayen kiwo da hanyoyin dabbobi ne ya kasance daya daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa rikice-rikice tsakanin makiyaya da manoma.
Ya kuma yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa fitar da umarnin zartarwa da ya haramta sayarwa, rabawa ko sauya fasalin filayen kiwo da hanyoyin dabbobi ba bisa ka’ida ba.
yace “MACBAN na matukar godiya ga gwamnatin jihar saboda sauraron korafe-korafenmu na dogon lokaci dangane da sayarwa da mamaye filayen kiwo da hanyoyin dabbobi ba bisa ka’ida ba,” in ji shi.
Ya kara da cewa an kafa kwamitin masu ruwa da tsaki da ya kunshi shugabannin kananan hukumomi, hakimai, jami’an filaye, wakilan makiyaya daga kowace karamar hukuma da shugabannin Miyetti Allah.
A cewarsa, kwamitin ya gudanar da bincike cikin gaskiya da adalci, inda wakilan makiyaya suka nuna filayen kiwo da hanyoyin dabbobi da ake zargin an sayar ko aka mamaye a cikin shekaru biyu da suka gabata. Daga bisani, hakimai da jami’an filaye suka tabbatar da bayanan kafin a rubuta su a hukumance.
Bakoji ya ce ta wannan hanya ne aka gano filayen kiwo da hanyoyin dabbobi guda 371 da suka fuskanci matsalar mamaya ko sauya amfani a cikin shekaru biyun da suka gabata, duk da dokokin gwamnati da aka kafa domin kare su.
Ya jaddada cewa wannan shiri ba wai don fifita wata kabila ko wata sana’a ba ne, sai dai domin hana rikice-rikice, karfafa zaman lafiya da tabbatar da tsaro a fadin Jihar Kano.
A nasa bangaren, shugaban FULDAN na Kano, Sani Adamu, ya bukaci Ma’aikatar Kula da Dabbobi ta tabbatar da aiwatar da wannan mataki yadda ya kamata, yana mai cewa hakan zai hana wasu manoma komawa wuraren da aka kwato.
Ya kuma yi gargadin cewa idan ba a dauki matakin da ya dace ba, wasu manoma na iya komawa wadannan wurare yayin da damina ke kara karatowa.
Shugabannin kungiyoyin biyu sun bayyana cewa warware matsalolin filayen kiwo da hanyoyin dabbobi ta hanyar doka da fahimtar juna zai taimaka wajen rage rikice-rikice, inganta tsarin amfani da kasa da kuma karfafa zaman lafiya tsakanin makiyaya da manoma a Jihar Kano.