Hari kan kyamar bakar fata. Gwamnatin Tarayya Za Ta Kwaso Fiye da ’Yan Najeriya 500 Zuwa Gida daga a Afirka ta Kudu
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta tantance tare da amincewa da kwaso fiye da ’yan Najeriya 500 da ke zaune a Afirka ta Kudu, waɗanda suka nuna sha’awar komawa ƙasar sakamakon hare-haren ƙyamar baƙi da ake ci gaba da yi.
Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Waje, Kimiebi Imomotimi Ebienfa, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja.
A cewarsa, bayanan da aka samu daga Ofishin Jakadancin Najeriya da ke Pretoria, Afirka ta Kudu, sun nuna cewa an tsawaita aikin tantance ’yan Najeriya da suka nemi a kwaso su zuwa ranar Laraba, 10 ga Yuni, 2026.
Ya ce kawo yanzu an riga an tantance tare da amincewa da fiye da mutum 500.
Ebienfa ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa ya amince da shirya jirage biyar na kwashe ’yan ƙasar, inda kamfanin jirgin sama na Air Peace zai gudanar da aikin.
Ya ƙara da cewa jirgi na farko, wanda ake sa ran zai ɗauki kusan fasinjoji 270, zai tashi daga Johannesburg a yammacin ranar Litinin, idan an samu dukkan izini da amincewar da ake buƙata domin gudanar da jirgin.
Haka kuma ya ce za a sanar da lokacin tashin jirgin da kuma lokacin isowarsa a Legas daga baya ta hannun Babban Ofishin Jakadancin Najeriya da ke Afirka ta Kudu.
Wannan mataki na zuwa ne bayan yawaitar hare-haren ƙyamar baƙi da suka shafi ’yan Najeriya da sauran baƙin ƙasashe da ke zaune a Afirka ta Kudu.