An Kashe Makiyayi Mai Shekara 15 Da Shanu 13 A Wani Sabon Hari A Plateau
Wani matashin makiyayi mai shekaru 15 mai suna Sadi Aliyu ya rasa ransa sakamakon wani hari da aka kai a yankin Sabon Gidan Kanar da ke Karamar Hukumar Jos ta Kudu a Jihar Plateau.
Shugaban kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) na Jihar Plateau, Ibrahim Yusuf Babayo, ne ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a Jos ranar Asabar.
Ya kuma bayyana cewa an kashe shanu 13 a harin, yayin da har yanzu ba a gano inda wasu shanu 11 suke ba.
A cewar Babayo, lamarin ya faru ne yayin da makiyayan ke kiwon dabbobinsu, inda wasu dauke da makamai suka kutsa yankin ba zato ba tsammani suka bude musu wuta.
Ya yi Allah-wadai da harin, yana mai cewa an kai shi ne ba tare da wani dalili ko tsokana ba.
“Marigayin tare da abokan aikinsa suna kiwon shanu lokacin da maharan suka farmake su. Sun kashe makiyayi guda daya tare da shanu 13, yayin da har yanzu ake neman wasu shanu 11 da suka bata,” in ji shi.
Babayo ya ce ci gaba da kai hare-hare kan makiyaya da dabbobinsu abin damuwa ne matuka, kuma yana barazana ga zaman lafiya da tsaro a Jihar Plateau.
Ya kara da cewa an kai rahoton lamarin ga sashen ‘yan sanda na Bukuru B Division da kuma rundunar Operation Enduring Peace Sector 6 domin daukar matakin da ya dace.
Kungiyar MACBAN ta bukaci jami’an tsaro da su gudanar da cikakken bincike kan harin, su kamo wadanda suka aikata laifin tare da gurfanar da su a gaban kuliya.
Har ila yau, kungiyar ta yi kira ga gwamnatoci a matakai daban-daban da su dauki matakan kariya domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma ba tare da la’akari da kabila ko sana’ar mutum ba.
Ta kuma roki al’ummar Fulani da sauran wadanda abin ya shafa da su kasance masu bin doka da oda tare da gujewa daukar doka a hannunsu, suna barin hukumomin da abin ya shafa su gudanar da aikinsu.
Babayo ya jaddada cewa kungiyar MACBAN na ci gaba da goyon bayan zaman lafiya, tattaunawa da hanyoyin doka wajen warware matsaloli, amma ta nace cewa dole ne a tabbatar da adalci ga marigayi Sadi Aliyu da kuma sauran wadanda suka rasa rayukansu sakamakon tashe-tashen hankula a Jihar Plateau.
Dailytrust.com