ICPC Ta Ƙi Amincewa da ikrarin Janye Ƙorafin Dangote kan Tsohon Shugaban NMDPRA
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Ƙasa (ICPC) ta ƙi amincewa da buƙatar attajirin Afirka, Alhaji Aliko Dangote, na janye ƙorafin da ya shigar kan tsohon babban daraktan hukumar kula da harkokin man fetur ta ƙasa (NMDPRA), Injiniya Farouk Ahmed.
ICPC ta bayyana cewa ta riga ta fara bincike kan zarge-zargen da aka yi wa tsohon shugaban NMDPRA, kuma za ta ci gaba da gudanar da binciken bisa tanadin dokokin da suka kafa hukumar, ko da kuwa mai ƙorafin ya janye ƙarar.
A Wata sanarwa da kakakin hukumar, John Odey, ya fitar ta tabbatar da karɓar wasiƙa daga lauyoyin Dangote mai ɗauke da kwanan wata 5 ga Janairun 2026, wadda aka yi wa take da “Sanarwar Janye Ƙorafi kan Injiniya Farouk Ahmed, tsohon ACE/CEO na NMDPRA.”
Sanarwar ta bayyana cewa wasiƙar ta nuna cewar wata hukumar tsaro dabam ta riga ta karɓi batun. Sai dai ICPC ta jaddada cewa wannan ba zai hana ko dakatar da binciken da take gudanarwa ba.
Hukumar ta ƙara da cewa tana da cikakken ikon doka da alhakin bincike kan duk wani zargi da ya shafi cin hanci da rashawa, domin kare muradun jama’a da tabbatar da gaskiya da adalci a ƙasar nan.