Hukumar NCC da CBN sun kanmala shirinsu dan magance matsalar korafe korafe al,umma na cire musu kudi bayan sayen data ko kati.
Hukumar Sadarwa ta Ƙasa (NCC) tare da Babban Bankin Najeriya (CBN) sun kammala tsara wani sabon tsari da zai magance matsalolin da masu amfani da layukan waya ke fuskanta wajen siyan katin waya da data da ke fāɗuwa. Wannan tsari ya samo asali ne bayan Doguwar tattaunawa da NCC, CBN, kamfanonin sadarwa (MNOs), masu bayar da sabis na ƙarin ayyuka (VAS), bankuna (DMBs) da sauran masu ruwa da tsaki, sakamakon ƙaruwa da korafe korafen da ake yi na cire kuɗi ba tare da samun katin waya ko data ba.
A karkashin wannan sabon tsari, duk lokacin da aka cire kuɗin mai saye amma bai samu katin waya ko data ba, an wajibta a mayar masa da kuɗinsa cikin daƙiƙu 30, sai dai idan mu’amalar tana nan a matsayin pending wanda a irin wannan yanayi mayar da kuɗin zai iya ɗaukar awa 24. Haka kuma, an tanadi dokar SLA da za ta fayyace nauyin da ke kan bankuna da kamfanonin sadarwa wajen warware matsalolin, tare da tilasta musu sanar da abokan ciniki ta hanyar sakon SMS kan nasara ko fāɗuwar kowace mu’amala.
Daraktar kula da harkokin masu amfani a NCC, Malama Farida ta bayyana cewa an samar da wata babbar manhajar sa ido ta tsakiya da NCC da CBN za su rika amfani da ita domin bibiyar fāɗuwar mu’amaloli, gano wanda ke da laifi da kuma sa ido kan mayar da kuɗi a kan lokaci. Ta ce an riga an mayar wa ’yan ƙasa sama da Naira biliyan 10 kuɗaɗensu na mu’amalolin da suka fāɗi, kuma ana sa ran fara aiwatar da wannan tsari daga ranar 1 ga watan Maris na shekarar 2026, bayan kammala amincewar hukumomi da haɗa dukkan tsarin fasaha.