Shugaban karamar hukumar nasarawa ambasada yusuf ogan boye yaraba tallafi ga matasan karamar hukumar.
Shugabancin karamar hukumar Nassarawa ya jaddada kudirinsa na ci gaba da tallafawa ‘ya’yan karamar hukumar Nassarawa da tallafin da za su dogara da Kawunansu.
Shugaban karamar hukumar ta Nassarawa Ambasada Yusuf Imamu Ogan boye ne ya jaddada Hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai yayin ba da tallafin babura da kekunan Dinki da Kudaden ga Yan asalin karamar hukumar Wanda ya gudana a helkwatar karamar hukumar.
Ya kuma Bayyana cewar, karamar hukumar Nassarawa za ta ci gaba da bayar da irin wannan kabakin arziki da sharbar roman damakaradiyya ga dukkanin Yan asalin karamar hukumar.
Ya bayyana cewar makasudun daya sanya karamar hukumar Nassarawa karkashin jagorancinsa ta ba da wannan tallafi shine, domin matasa su samu damar tsayawa da kafafuwansu ta hanyar ba da jari da sauran su.
Ambasada Yusuf Ogan boye ya yi kira ga sauran matasa maza da mata Wadanda basu samu wannan kabakin arziki ba, da su kwantar da hankulansu domin su ma nasu yana tafe nan da zuwa wani Dan lokacin.
Shugaban karamar hukumar ya kuma kara kira ga alummar karamar hukumar Nassarawa da sauran alummar jihar Kano, da su ci gaba da baiwa Shugabancin Gwamnan Kano injiniya Abba Kabir Yusuf goyan baya domin ya samu damar bijiro da ayyukan raya kasa a ciki da wajen jihar Kano.
Haka zalika Shugaban ya yi alkawarin cewa, hukumar gudanarwar karamar hukumar tana Nan tana bincikawa lunguna da sako domin lalibo mutanen da suka cancanta a basu wanann tallafi da taimakawa marasa karfi Yan asalin karamar hukumar Nassarawa.
Bugu da kari, Shugaban ya bukaci Wadanda suka amfana da tallafin babura da kekunan Dinki da Kudaden da Kuma mota, da su yi amfani da su ta hanyar da ta dace yadda za su taimakawa wasu a nan gaba.
A jawabisa Musa Wanda aka fi sani da dankyas ya samu mota da babur, inda Kuma ya bayyana Jin dadinsa dangane da wannan tallafi da Shugaban karamar hukumar Nassarawa Ambasada Yusuf Imamu Ogan boye ya bashi.
Musa dankyas ya bayyana cewar, ba zai taba mantawa da wannan kabakin arziki da Shugaban karamar hukumar ya bashi, Inda Kuma, yayi alkawarin ci gaba da yada munufofin Shugaban karamar hukumar tare da Gwamnan Kano injiniya Abba Kabir Yusuf.
Musa dankyas ya yi kira ga alummar karamar hukumar Nassarawa da suke a cikin kwacce jam’iyya da su a wannan tafiyar da su a cikin jamiyyar APC domin kofarsu har yanzu a bude take.
Shi ma a nasa bangaren Isyaku baban Aisha Wanda ya rabauta da Kudaden naira dubu dari biyar domin kafa jarin, yayi mutukar nuna gadiyarsa ga wannan kudade da ya samu don Samar da wata sana”a da dogara da kansa.
Isyaku baban Aisha ya shawarci alummar karamar hukumar Nassarawa da su ci gaba da yiwa Shugaban karamar hukumar Ambasada Yusuf Imamu Ogan boye Addu’ar Allah ya ci gaba da taimaka masa wajen jagorancin alumma cikin nasara, inda Kuma ya Sha alwashin ci gaba da yada manufofin jam’iyyar APC ta jihar Kano karkashin jagorancin Gwamnan jihar Kano injiniya Abba Kabir Yusuf.
Daga karshe sun godewa Gwamnan Kano injiniya Abba Kabir Yusuf bisa yadda yake baiwa Shugabancin karamar hukumar Nassarawa cikakken hadin Kai yadda ya kamata.