Ma,aikatar wajen Najeriya tayi gargaɗi kan wasu masu daukan aiki dan yaki da kasashen waje
Ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta nuna fargaba kan abin da ta kira ƙaruwar ƴan ƙasar da ake ɗauka aiki ba bisa ƙa’ida ba domin yaƙi a ƙasashen waje.
A cikin wata sanarwa aka fitar ranar Lahadi, mai magana da yawun ma’aikatar Kimiebi Imomotimi Ebienfa ya ce: “’Yan Najeriya da dama da suka fada cikin irin wannan yanayi mara daɗi an tura su zuwa fagen daga bayan an yaudare su tare da tilasta musu sanya hannu kan kwangilolin aikin soja.”
Jami’ai sun ce bincike da rahotannin tsaro sun nuna cewa an yaudari wasu ƴan Najeriya da alƙawuran samun ayyuka yi masu gwaɓi, ko damar yin karatu cikin sauki.
A farkon makon nan ne hukumomin ƙasar Ukraine suka ce jami’an leƙen asirin sojinta sun gano gawarwakin wasu ƴan Najeriya guda biyu a yankin Luhansk.
Sun ce duka mutanen biyu sun sanya hannu kan kwangiloli da rundunar sojin a shekarar 2025, kuma an tura su yankunan da aka mamaye ba tare da wani horo na soja ba.
A cewar Ukraine, an kashe su ne a ƙarshen watan Nuwamba a lokacin da suke yunƙurin kutsa kai cikin yankunan Ukraine.