Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubukar ya nuna damuwarsa kan karancin fitowar jama,a. A zaben kananan hukumomi a babban birnin tarayya abuja a ranar asabar
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya nuna damuwa kan ƙarancin fitowar jama’a a zaɓen Ƙananan Hukumomin Babban Birnin Tarayya da aka gudanar ranar Asabar, yana mai cewa hakan alama ce da ke nuna dimokuraɗiyya na shaƙewa a ƙasar.
A wata sanarwa da ofishinsa ya fitar, Atiku, wanda jigo ne a jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), ya bayyana ƙarancin fitowar a matsayin hukunci mai tsauri kan yanayin dimokuraɗiyyar Najeriya a ƙarƙashin gwamnati mai ci.
Ya ce irin wannan ƙarancin halartar zaɓe a babban birnin ƙasa ba abu ne da ya faru haka kawai ba, sai dai sakamakon yanayin siyasa da ya gurbace ta hanyar rashin haƙuri, tsoratarwa, da kuma raunana muradun ’yan adawa.
A cewarsa, gwamnatin da ke mulki ta rungumi manufofin da ke takaita sararin dimokuraɗiyya, da tsangwamar masu adawa, da matsa lamba ga masu sauya sheƙa, tare da haifar da yanayi inda ake kallon ra’ayoyin siyasa na daban a matsayin barazana maimakon gudummawa ga ci gaban ƙasa.
“Atiku ya ce, idan ’yan ƙasa suka rasa amincewa cewa ƙur’unsu na da tasiri, to dimokuraɗiyya na fara mutuwa.”
Ya ƙara da cewa abin da ake gani ba kawai sakacin masu zaɓe ba ne, illa sakamakon salon mulki da ke takura wa jam’iyyun adawa da ra’ayoyi mabambanta.
Ya yi gargaɗi cewa idan aka bar wannan yanayi ya ci gaba, zai iya janyo mummunar illa ga tsarin dimokuraɗiyya da aka shafe shekaru ana ginawa.
A ƙarshe, ya yi kira ga jam’iyyun adawa da sauran masu kishin dimokuraɗiyya da su haɗa kai domin kare Jamhuriya da sake gina Najeriya.