Babbar Alkaliyar Najeriya, Kudirat Kekere-Ekun, za ta rantsar da sabon Alkalin Kotun Koli, Joseph Olubunmi Kayode Oyewole, a ranar Laraba, 25 fabureru

Bikin rantsuwar  Zai  gudanar ne   a Kotun mai  Lamba Biyu   da ke harabar Supreme Court of Nigeria a Abuja da misalin ƙarfe 2 na rana, inda ake sa ran manyan alkalai za su halarta.

 

 

 

 

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kujerun Kotun Kolin sun ragu a baya-bayan nan sakamakon ritayar wasu alkalai da suka kai shekarun ritaya kamar yadda doka ta tanada.

 

 

Bincike ya nuna cewa kafin ɗaukaka shi zuwa Kotun Koli, Mai Shari’a Oyewole ya taɓa zama Alkalin Kotun Ɗaukaka Ƙara tare da riƙe muƙamin Shugaban Sashen Enugu na Kotun Ɗaukaka Ƙara a Jihar Enugu.

 

 

 

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Kotun Koli, Festus Akande, ya fitar a ranar Lahadi.

 

 

 

Akande ya bayyana cewa sabon alkalin zai kawo ƙwarewarsa da mutuncinsa wajen ƙara ƙarfafa ikon Kotun Koli domin yanke hukunci cikin adalci da kuma cikin lokaci.

 

 

 

Ya ƙara da cewa naɗin Oyewole ya nuna jajircewar ɓangaren shari’a na Najeriya wajen tabbatar da bin doka, samar da adalci da kuma ƙarfafa kotu da gogaggun alkalai masu ƙwarewa da jajircewa.

 

 

 

Kotun Kolin Najeriya ta jaddada aniyarta na ci gaba da tsayawa kan turbar adalci, gaskiya da ’yancin cin gashin kai na ɓangaren shari’a domin amfanin dukkan ’yan Najeriya.

 

 

 

A cewarsa, wannan rantsarwa wata sabuwar hanya ce ta farfaɗo da ɓangaren shari’a tare da tabbatar da ci gaba da gudanar da adalci bisa manyan ƙa’idojin gaskiya, ƙwarewa da rashin son kai.

 

 

 

 

Haka kuma, ya buƙaci duk baƙin da aka gayyata da su bi ƙa’idoji da matakan tsaro na kotu yadda ya kamata.

You might also like
Leave a comment