Ƙasashen Larabawa sunyi allah wadai kan kalaman jakadan Amurka a Isra’ila
Gwamnatocin ƙasashen Larabawa da na Musulmi sun yi alla-wadai da kalaman jakadan Amurka a Isra’ila Mike Huckabee, wanda ke nuni da cewa Isra’ila za iya mamaye yanki mai faɗin gaske a gabas ta tsakiya bisa hujjar Littafin Injila.
A wata hira da wani mai sharhi na Amurka mai ra’ayin mazan jiya Tucker Carlson, an tambayi Huckabee ko Isra’ila na da ƴancin mallakar wani yanki da aka bayyana a matsayin “Gabas ta tsakiya baki ɗaya”.
Jakadan ya ce “zai yi kyau idan ta kwashe duka”.
Amma ya ƙara da cewa Isra’ila ba ta neman yin hakan, amam ta na “neman aƙalla ta ci gaba da riƙe ƙasar da ta riga ta mamaye” da kuma kare al’ummarta.
A cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da suka fitar, fiye da gwamnatoci goma da suka haɗa da Jordan da Masar da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, sun kira kalaman “masu haɗari da tayar da hankali”, da kuma barazana ga yunƙurin kawo ƙarshen yaƙin Gaza.