Wata Guguwa a madagaska ta kashe aƙalla mutum 35

Aƙalla mutun 35 ne suka mutu bayan da wata guguwa mai ƙarfin gaske ta afka wa Madagascar, a cewar hukumar taƙaita afkuwar bala’o’i ta ƙasar.

 

 

 

Guguwar mai suna Gezani ta afka ne ranar Talata, inda ta lalata abubuwa a tashar jiragen ruwa da ke Toamasina.

 

 

 

Ofishin takaita afkuwar bala’i ta Madagascar ta ce an samu “gagarumin ruɗani” – tare da ruwaito faɗuwar gidaje a yankin da kuma gano gawawwaki.

 

 

 

 

Al’ummomi sun shiga cikin duhu sakamakon katsewar lantarki, yayin da itatuwa suka yi ta tuge wa suna faɗi ƙasa.

 

 

 

Mutane sama da 250,000 ne lamarin ya shafa ko kuma ya ɗaiɗaita, a cewar ministan kula da muhalli ta ƙasar Max Fontaine yayin tattaunawa da BBC.

You might also like
Leave a comment