Hukumar FRSC ta sallami jami’aita 43 saboda rashin kulawar aiki
Hukumar kiyaye afkuwar haɗura ta ƙasa FRSC ta ɗauki matakin ladabtarwa mai tsauri inda ta sallami jami’ai 43 daga aiki sakamakon rashin biyayya da ɗabi’a maras kyau, wanda laifuka ne da suka aikata yayin aiki.
Sanawar da hukumar ta fitar ta ce “Daga cikin waɗannan jami’an, 31 an sallame su ne saboda rashin biyayya, 5 saboda ɗabi’a maras kyau, sannan 7 saboda aikata laifuka yayin sintiri.”
Shugaban FRSC, Shehu Mohammed ya bayyana wannan mataki a matsayin abu da aka yi don tabbatar da cewa jami’ai sun bi ƙa’idar aiki yadda ya kamata.
Ya ce “alamar FRSC alama ce ta ɗabi’a da ɗawainiya, kuma kowane jami’in da ya saba wa ƙa’idojin hukumar zai fuskanci hukunci.”
Ya ƙara da cewa rashin biyayya babban laifi ne musamman ga hukumar da aka ɗora wa alhakin kare rayukan mutane a hanyoyi, yayin da ɗabi’a mara kyau da aikata laifuka yayin sintiri ke rage amincin jama’a gare su da kuma sabɓa wa ka’idojin hukumar da suka haɗa da gaskiya da ladabi.
Hukumar ta ce za ta ci gaba da ƙara lura da ayyukan cikin gida da karfafa tsarin kulawa, da kuma wayar da kan jami’ai kan ɗabi’a mai kyau a dukkan sassan hukumar a faɗin ƙasa.