Kamfanin KEDCO ya koka kan matsalolin wutar a jihohin Arewa maso Yamma

Kamfanin rarraba wutar lantarki na Kano, KEDCO, ya bayyana matukar damuwa kan matsalolin da ke shafar samar da wuta daga Kamfanin Wutar Lantarki na Najeriya da kuma kamfanin rarraba wutar ta ƙasa TCN zuwa jihohin Arewa maso Yamma.

 

 

 

 

Kamfanin ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta umarci TCN da  yabayar da  muhimmanci ga manyan ayyukan layin wutar lantarki da gyare gyare domin inganta isar da wuta a yankin.

 

 

 

 

KEDCO ya ce “a halin yanzu hanyoyi biyu kacal ne ke kai wuta zuwa cibiyar Kano wato ta Kaduna da Jos kenan, lamarin da ya rage ƙarfin tsarin samar da wuta da kuma sa shi cikin hadarin katsewa idan matsala ta faru a daya daga cikin hanyoyin. ”

 

 

 

 

Ya ƙara da cewa akwai buƙatar ƙara tsaro da gyara da kuma faɗaɗa ƙarfin layin wutar Shiroro zuwa Mando har zuwa Kano domin rage yawan ɗaukewar wuta.

 

 

 

 

Kamfanin ya ƙara da cewa a makonnin baya bayan nan ana yawan samun katsewar wuta a ƙarshen mako sakamakon ayyukan gyara da ake yi a layukan wuta, musamman aikin girka sabbin na’urorin OPGW.

 

 

 

A cewarsa “wannan na matuƙar shafar harkokin masana’antu da rayuwar al’umma a jihohin yankin da kuma yankunan da yake aiki.

 

 

 

 

Don rage tasirin matsalar, KEDCO ya ce yana aiki tare da Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya da kuma Hukumar Tsarin Wutar Lantarki domin inganta daidaito a hidimar wuta.

 

 

 

 

Ya kuma bayyana cewa tana hanzarta shirye shiryen faɗaɗa samar da wuta a cikin gida domin rage dogaro gaba ɗaya ga cibiyar lantarki ta kasa.

You might also like
Leave a comment