Hukumar shige da fice ta nigeria ta miƙa mata shida da aka ceto daga masu safarar mutane ga hukumar NAPTIP ta kasa rashen jahar Kano
Hukumar Shige da Fice ta Najeriya (NIS) ta ceto mata shida da ake zargin an yi yunkurin safarar su zuwa ƙasar Masar ta hannun filin jirgin sama na Malam Aminu Kano da ke Kano.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar NAPTIP shiyyar Kano, Mohammed Habeeb ya fitar, ya ce an miƙa waɗanda aka ceto ga Hukumar Hana Safarar Mutane (NAPTIP) domin ba su kulawa, da shawarwari da kuma gyara rayuwa.
An ceto matan ne yayin wani samame da jami’an NIS suka gudanar. Ana zargin suna kan hanyarsu ta zuwa birnin Alkahira (Cairo) na ƙasar Masar. Sai dai wanda ake zargi da shirya tafiyar ya tsere, yayin da aka kama manajan wani otel domin ci gaba da bincike.
A yayin tambayoyi, matan sun bayyana cewa an yaudare su ne da alkawarin samun “rayuwa mai kyau” a ƙasashen waje. Sun ce waɗanda suka shirya tafiyar ne suka ɗauki nauyin dukkan kuɗaɗen tafiyar, amma da sharadin cewa za su biya kuɗin da riba bayan sun isa inda za su je sun fara aiki.
Hukumar NAPTIP ta shiyyar Kano ta karɓi matan tare da samar musu da matsuguni domin ba su shawara da kuma taimaka musu su farfaɗo da rayuwarsu, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin cafke sauran waɗanda ake zargi da hannu a lamarin