Al’ummar Tudun Wada/Doguwa Sun bukaci Dr umar suleman umar (DRUSU )Ya Wakilce Su a Majalisar Ƙasa
Al’ummar ƙaramar hukumar Tudun Wada/Doguwa, daga garin Malan da ma sauran yankuna, sun bayyana amincewarsu da Dr. Umar Suleiman, wanda aka fi sani da DRUSU, domin ya wakilce su a Majalisar Tarayya.
Wannan amincewa ta fito ne a yayin wani gangamin fitar da dandazo, maza da mata, da yara da manya, suka fito ƙwansu da ƙwarkwatarsu domin nuna goyon baya da sha’awarsu ga DRUSU a matsayin wanda za su ba dama ya wakilce su a matakin ƙasa.
A yayin taron, al’ummar yankin sun bayyana irin gagarumar gudummawar da DRUSU ke bayarwa wajen ciyar da yankin gaba, musamman ta fannonin ilimi, lafiya, noma da kiwo, wasanni, da kuma walwalar yara da matasa.
Inda Suka ce irin waɗannan ayyuka ne suka sa suka yarda cewa shi ne ya fi dacewa da wakiltar muradunsu.
Wannan shaidar ta fito ne daga wakilan DRUSU da ke kula da aiwatar da ayyukan alkhairi a yankunan daban-daban, inda suka jaddada cewa ayyukan suna gudana cikin gaskiya da haɗin kan al’umma.
Haka kuma, al’ummar mazaɓun yankin baki ɗaya, tare da wakilan jam’iyyu daban-daban, sun yi masa mubaya’a ba tare da wata adawa ba, lamarin da ke nuna cikakken goyon baya da haɗin kai daga ɓangarori daban-daban.
Masu ruwa da tsaki sun bayyana cewa wannan goyon baya babbar alama ce ta yadda al’umma ke neman shugabanci nagari, mai hangen nesa, da kishin ci gaban jama’a a Majalisar Tarayya
Dandazon al,ummar sun kai ziyarar nuna goyon bayan zuwa gidan iyayensa dan rokonsu da rokar musu drusu da ya amince da bukatar Al,ummar ta tudun wada da doguwa ya musu takarar majilisar tarayya.