Wasu fusatantun mutane sun harbe wani Jami’in. Civil defence har lahira (NSCDC) a Jihar Rivers

Wani jami’i na rundunar Nigeria Security and Civil Defence Corps (NSCDC) daga sashen Special Mining Marshal ya mutu bayan an harbe shi a ranar Litinin a ƙauyen Umunwantu Village, cikin al’ummar Umuechem Community da ke ƙaramar hukumar Etche Local Government Area a Rivers State.

 

 

 

 

 

 

Rahotanni sun ce jami’in yana cikin tawagar Special Mining Marshal da aka turo daga hedikwatar civil defence   ta ƙasa domin gudanar da aiki a yankin.

 

 

 

 

An ce ya raka wasu jami’an gwamnati da suka je aiwatar da dokar haramta tono yashi (sand dredging) a yankin.

 

 

 

 

 

 

Sai dai lamarin ya rikide zuwa rikici tsakanin direbobin manyan motocin ɗaukar yashi  da jami’an gwamnati, bayan bindigar jami’in ta tashi bisa kuskure ta kashe wani mutum mai suna Bright a wurin da ake zubar da yashi.

 

 

 

 

 

Mazauna yankin sun shaida wa jaridar Daily Trust cewa bayan wannan hatsari, wasu da ake zargin ‘yan daba ne sun kai wa jami’in hari tare da harbe shi har lahira a wurin.
Wani babban jami’i na rundunar NSCDC a Rivers  ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya bukaci a sakaya sunansa, yana mai cewa jami’in da abin ya shafa an turo shi ne daga hedikwatar ƙasa.

 

 

 

 

 

 

Bayan faruwar lamarin, shugaban Etche Local Government Area, Chief Chima Njoku, ya ba da umarnin dakatar da dukkan ayyukan direbobin tipper da wuraren ajiyarsu a yankin har sai an bayar da wani sabon umarni.

 

 

 

 

 

A cikin sanarwar da sakataren yaɗa labaransa Dagogo Isaac ya fitar, an umurci shugabannin ƙungiyoyin direbobin tipper a yankin da su gaggauta zuwa ofishin ‘yan sanda na Okehi Police Division domin su bayyana rawar da suka taka ko bayanin abin da ya jawo toshe hanyar Chokocho–Igwuruta Federal Highway.
Tun da farko ma’aikatar Federal Ministry of Mines and Steel Development ta haramta aikin tono yashi a wasu hanyoyi da al’ummomi a yankin, saboda matsalolin muhalli da lalacewar hanyoyi da ayyukan ke haifarwa.

You might also like
Leave a comment