ƴansanda sun mamaye kasuwar Onitsha bayan umarnin gwamna na rufe kasuwar tsawon mako guda

Rundunar ƴansandan jihar Anambra ta ce ta tura jami’anta zuwa babbar Kasuwar Onitsha biyo bayan umurnin gwamnan jihar, Chukwuma Soludo na rufe kasuwar na tsawon mako guda.

 

 

 

Gwamnan ya ba da umarnin rufe kasuwar ne saboda ƴan kasuwar na bin dokar hana fita da mayaƙan IPOB ke sakawa a kowace ranar Litinin.

 

 

 

Kasuwar dai ana ganin ita ce mafi girma a Yammacin Afirka.

 

 

 

Rundunar ta ce ta tura ƴansandan ce “don tabbatar da doka da oda da kuma hana duk wani abu da zai kawo tashin hankali a cikin jama’a.”

 

 

 

Rahotanni da bidiyo da aka yaɗa a kafafen sada zumunta sun nuna ‘yan kasuwa da jama’a suna gudu sakamakon harbe-harbe.

 

 

 

Wannan mataki na gwamnan na zuwa ne bayan da ‘yan kasuwa da dama a wannan kasuwar suka zaɓi ci gaba da rufe shagunansu duk kuwa da tabbacin da aka bayar na inganta tsaro da kiran a farfaɗo da buɗe shaguna.

 

 

 

 

Shekaru da dama, ana rufe kasuwanni da makarantu da ofisoshin gwamnati a kowace Litinin a wasu birane da garuruwa a yankin, bisa umarnin ƴan IPOB.

 

 

 

 

You might also like
Leave a comment