Da Dumi Dumi: Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Tabbatar da Hukuncin da Ya Hana INEC Amincewa da Taron PDP na Ibadan
Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta tabbatar da hukuncin da Kotun Tarayya ta yanke a Abuja, wanda ya hana Hukumar Zaɓe ta Ƙasa Independent National Electoral Commission (INEC) amincewa da babban taron jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da aka gudanar a Ibadan a ranakun 15 da 16 ga Nuwamba, 2025.
A hukuncin da ta yanke a ranar Litinin, kwamitin alkalai uku na kotun ɗaukaka ƙarar ya yi watsi da ƙarar da jam’iyyar PDP ta shigar, wadda ke kalubalantar ikon Kotun Tarayya ta Abuja na sauraron shari’ar.
Kotun ta bayyana cewa Kotun Tarayya tana da cikakken ikon sauraron shari’ar, inda ta yi watsi da hujjar ɓangaren da Adamu Turaki ke jagoranta, wanda ya ce rikicin lamari ne na cikin gida na jam’iyyar kawai.
Saboda haka, kotun ta tabbatar da hukuncin da aka yanke tun farko na hana amincewa da taron jam’iyyar da aka gudanar a Ibadan.