Gwamnatin jahar Kano Ta Amince da Ayyukan Ci Gaba da suka kai Naira Biliyan 310 a Sassa Daban-daban na fadin jahar.

Majalisar Zartarwa ta Jihar Kano ta amince da ayyuka da shirye-shirye da kudinsu ya haura Naira biliyan 310, domin inganta ababen more rayuwa, ilimi, lafiya, gidaje, da sauran muhimman fannoni a fadin jihar.

 

 

 

 

 

An cimma wannan matsaya ne a taron Majalisar Zartarwa na 38 da gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, ya jagoranta a dakin taro na Government House Kano.

 

 

 

 

 

Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida na jihar, Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa bayan kammala taron.

 

 

 

 

 

A cewar sanarwar, majalisar ta tattauna kan muhimman batutuwan gudanar da gwamnati kafin ta amince da ayyuka da kudinsu ya kai N310,266,203,046, wanda zai shafi sassa da dama na tattalin arzikin jihar.
Fannin Ilimi

 

 

 

A bangaren ilimi, majalisar ta amince da:
Naira miliyan 238.02 domin sayen fom na jarabawar UTME na Joint Admissions and Matriculation Board ga dalibai da suka  cancanta a fadin jihar.

 

 

 

Gyaran makarantar Government Girls Secondary School Hotoro  a karamar hukumar Nassarawa.
Gyaran makarantu a Bagwai LGA da yankin Kofar Nassarawa.
Biyan kudin masu samar da abincin daliban makakwanan   kwana.
Sayen littattafan karatu ga dalibai a dukkan kananan hukumomi 44 na jihar.

 

 

 

sai kuma Gina makarantar makiyaya a Dambatta LGA.
Ayyukan Hanyoyi da Ababen More Rayuwa
A karkashin Ma’aikatar Ayyuka da Gine-gine:

 

 

Gyaran hedikwatar Kano State Fire Service.
Kammala ginin Masallacin Juma’a a Nassarawa.
Karin aiki a Hasiya Bayero Paediatric Hospital.
Gyaran Rimin Auzinawa Road a Ungoggo.
Gina hanyoyin Ladanai road network.
Ware N13.2 biliyan domin ayyukan mazabu na shekarar 2026.

 

 

 

Haka kuma an amince da:
Gyaran hanyar da ta taso daga Gidan Malam Aminu Kano ta bi ta Tal’udu, Gadon Kaya, Yahaya Gusau zuwa Sharada.
Sake gina hanyar Race Course Extension zuwa Audu Bako Way da sauran hanyoyi a Nassarawa.

 

 

 

bangaren Ci gaban Karkara kuma
Majalisar ta amince da gina hanyoyin karkara (feeder roads) a kananan hukumomi kamar:
Gezawa
Bichi
Garko
Takai
Domin saukaka zirga-zirga da kasuwanci a karkara.

 

 

Bangaren Lafiya da Ruwa
Sayen na’urorin dialysis ga Abubakar Imam Urology Centre.
Sayen kayan aikin hakori ga cibiyoyin lafiya.
Biyan bashin wutar lantarki ga tashoshin tace ruwa guda biyar da ake bi bashin  Kano Electricity Distribution Company.

 

 

 

Babban Shirin Gidaje
Majalisar ta amince da sama da Naira biliyan 113 domin gina gidaje 480 a Rijiyar Gwan-Gwan, a karkashin shirin Gida Gida Mega City na Ma’aikatar Gidaje.

 

 

Sauran Ayyuka
ta kuma amince da
Gina cibiyar Emergency Operations Management Centre a Government House.
Biyan diyya ga wadanda aikin layin wutar 330KVA na Transmission Company of Nigeria zai shafa.
Gina magudanar ruwa a Kurnar Asabe a karamar hukumar Dala.

 

 

 

Samar da tsirrai miliyan 10 domin shirin dashen bishiyoyi na 2026.
Tsawaita layin wutar lantarki a hanyar Bunkure Road.
Naira biliyan 1.34 domin shirin ciyarwa na watan Ramadan na 2026.

 

 

Matakan Manufofi
Majalisar ta kuma amince da:
Kwangilar gina AKK Industrial Parks.
Gyaran motocin shirin Girl Child Initiative.
Yin allurar rigakafi ga tumaki da awaki a dukkan kananan hukumomi 44.
Haka kuma majalisar ta amince a gyara dokokin:
Kano State Private and Voluntary Institutions Board Law 2014
Kano State Electricity Bill 2026
Domin turawa zuwa Majalisar Dokokin Jihar Kano domin tantancewa.

 

 

Bugu da kari, majalisar ta lura da sake fara aiki da tashar wutar lantarki ta Tiga Hydropower Plant mai karfin 2MW + 8MW bayan shekaru tana tsaye.

 

 

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa wadannan matakai na nuna kudurin gwamnatin gwamna Abba Kabir Yusuf na inganta rayuwar al’ummar Kano, samar da ayyukan ci gaba, da kyautata ayyukan gwamnati a jihar.

You might also like
Leave a comment