Gwamnatin Kano Ta kafa kwamitin wayar da kan jama’a kan Rajistar Zaɓe

Gwamnatin Jihar Kano ta ƙara ƙaimi wajen wayar da kan al’umma domin ƙara yawan mutanan da sukayi rajistar zaɓe, inda take da burin ganin sama da miliyan goma sunyi register zabe afadin jahar kano  kafin zaben shekara ta 2027

 

bayanin haka ya fito daga bakin Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, inda  bayyana cewa daga watan Agustan 2025 zuwa yanzu, mutane 267,790 sun kammala rajistar zaɓe kuma suna jiran karɓar katin zaɓensu (PVC).

 

 

Ya ce gwamnatin jihar ta kafa kwamitin wayar da kai mai ƙarfi domin ƙarfafa rajistar zaɓe da karɓar PVC, wanda ke da wakilan ma’aikatu da ƙungiyoyi daban-daban, tare da nufin kai saƙo zuwa dukkan ƙananan hukumomi Jahar kano 44

 

 

Waiya ya kuma bayyana cewa gwamnati na aiwatar da sama da ayyuka 900 a faɗin jihar, inda ya buƙaci al’ummar Kano su ci gaba da marawa gwamnati baya domin ci gaban dimokuraɗiyya da walwalar jama’a.

 

yakuma ja hankalin al,ummar jahar kano da su cigaba da yiwa gwamnatin injiniya Abba kabiru Yusuf  Adu,oi dan ganin ya cimma manyan ayyukan cigaban jahar kano da yasa agaba.

You might also like
Leave a comment