Inuwa Waya na taka muhimmiyar rawa wajen sauƙaƙa sauyin sheƙar gwamnan kano Abba kabir yusuf zuwa APC — Kakakin APC na Kano

Tsohon ɗan takarar gwamnan Jihar Kano a ƙarƙashin jam’iyyar APC, Alhaji Inuwa Waya, na taka rawa sosai wajen sauƙaƙa sauyin sheƙar da ake shirin yi na Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, daga jam’iyyar NNPP zuwa APC.

Kakakin jam’iyyar APC a Kano, Honarabul Ahmed Arewa, ne ya bayyana hakan a cikin wani bidiyon tattaunawa (video podcast) da aka yi a Kano.

Ya ce:

“Ko da yake na taɓa gaya muku cewa akwai wasu mutane da ke ƙoƙarin jawo Abba zuwa APC, amma zan keɓe Inuwa Waya in gaya muku yadda yake ƙoƙarin shigar da gwamnan cikin jam’iyyarmu tare da ba shi damar gudanar da aikinsa yadda ya kamata,” in ji Arewa.

Ya ƙara da cewa:

“Wannan mutum (Inuwa Waya) babban mutum ne da muke alfahari da shi a APC, saboda hangen nesansa da kuma bin ka’idojin ci gaban al’umma, tare da goyon bayan ‘ya’yan jam’iyyar APC a Kano.”

A cewar Aruwa:

“Ba wai batun sauyin sheƙar Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa APC kaɗai ba ne, Mai Girma Inuwa Waya na kuma ba da shawarwari kan yadda, idan gwamnan ya shiga APC, zai zauna lafiya tare da aiwatar da manyan ayyukan ci gaba a faɗin Jihar Kano.”

Kakakin APC a Kano ya kuma bayyana nasarorin da aka samu a lokacin da Inuwa Waya ya tsaya takarar gwamna a ƙarƙashin APC, yana mai cewa idan Alhaji Abba Kabir Yusuf ya shigo APC, waɗannan nasarorin za su ƙaru sosai.

Haka kuma, ya yaba masa bisa saurin ɗaukar matakai wajen bunƙasa APC a Kano, yana mai cewa idan gwamnan ya shiga babbar jam’iyyar siyasa mafi girma a Afirka (APC) kuma aka karɓi shawarwarinsa, to za a cimma sakamakon da ake buri.

You might also like
Leave a comment