Kungiyar kwadago NLC tace ma,aikatan ABuja bazasu koma bakin aikiba duk da umarnin da kotu tabayar na komawa aiki

Ƙungiyar kwadago  NLC, ta ce ma’aikatan  Babban Birnin Tarayya, Abuja  ba za su koma bakin aiki ba, duk da umarnin da Kotun Kwadago ta Ƙasa ta bayar.

 

 

A yau ne kotu ta umarci ma’aikatan da su dakatar da yajin aikin da suke yi, ta kuma ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 25 ga Maris, 2026.

 

 

Amma NLC ta ce wannan umarni ba zai hana su ci gaba da yajin aikin ba.

 

 

Ƙungiyar ta kuma soki Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, bisa barazanar korar ma’aikata daga aiki jim kaɗan bayan kotu ta fitar da umarninta.

 

 

Mukaddashin Babban Sakataren NLC, Benson Upah, ya ce kotu ba ta yi magana  game da matsalolin da ma’aikatan ke fuskanta, musamman rashin tura kuɗaɗen fansho da kuma kuɗaɗen gida, wato National Housing Fund, da ake cirewa daga albashinsu.

 

 

Ya ce idan ana tunanin wannan umarni zai karya gwiwar ma’aikata, to hakan ba zai yiwu ba, domin sun kuduri aniyar ci gaba da fafutuka har sai an biya musu haƙƙinsu.

 

 

NLC ta kuma gargadi duk wata hukuma da ke ƙin bin dokokin fansho da na National Housing Fund, cewa za su ɗauki mataki a kansu.

You might also like
Leave a comment