Rundunar yan sadan babban birnin tarayya ta dakile yukurin fashi da makami a yankin kado da ke abuja

Rundunar ’Yan Sanda ta Babban Birnin Tarayya (FCT) ta ce ta daƙile wani yunƙurin fashi da makami a yankin Kado da ke Abuja, inda ta kama mutum ɗaya tare da ƙwato makamai da wasu kayayyaki da ake zargin na masu laifi ne.

 

 

A cewar wata sanarwa da jami’ar hulɗa da jama’a ta rundunar, SP Josephine Adeh, ta fitar a ranar Litinin, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 6:15 na safiyar Juma’a, 23 ga Janairu, 2026.

 

 

Sanarwar ta ce ofishin ’yan sanda na Mabushi ne ya samu kiran gaggawa cewa wasu mutane dauke da makamai na kai wa direbobi hari a kusa da gidan mai na MRS da ke Kado, lamarin da ya sa jami’an tsaro suka gaggauta kai ɗauki zuwa wajen.

 

 

Da isarsu wurin, mutanen da ake zargin su kusan uku ne sun yi yunƙurin tserewa bayan sun hango ’yan sanda, abin da ya haifar da artabu da musayar harbe-harbe.

 

 

A yayin artabun, ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi ya samu raunin harbin bindiga, inda aka kai shi asibiti domin samun kulawar likita, yayin da sauran suka tsere zuwa dazuka da ke kusa.

 

 

Rundunar ta ce ta ƙwato kayayyaki da dama daga wurin, ciki har da wata mota kirar Volkswagen Golf 2 mai launin baƙi mai lambar rajista JJJ 112 DW, wadda ake zargin masu laifin ke amfani da ita.

 

 

Sauran kayayyakin da aka ƙwato sun haɗa da bindigar Beretta guda ɗaya, bindiga ƙirar gida guda ɗaya, janareta ƙirar Firman, wayoyin hannu biyu, katin ATM na Access Bank, da kuma wasu kayayyaki da ake zargin ana amfani da su wajen aikata laifuka, ciki har da danƙon harbi (catapult), fensir na ƙarfe (pliers), takalma, huluna da wasu kayan sawa.

You might also like
Leave a comment