Shugaban hukumar NDLEA na kasa birgediya genar buba marwa mai ritaya ya baiyana nasarar da hukumar tasamu a shekaru biyar da suka gabata
Shugaban Hukumar Yaƙi da Tu’ammali da Safarar Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa, NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya, ya bayyana cewa cikin shekaru biyar da suka gabata, hukumar ta kama mutane akalla dubu saba’in da bakwai da dari bakwai da casa’in da biyu, 77,792, da ake zargi da tu’ammali da miyagun ƙwayoyi a faɗin Nijeriya.
Buba Marwa ya bayyana hakan ne a birnin Abuja, inda ya ce a tsawon shekarun, NDLEA ta kuma kama miyagun ƙwayoyi da nauyinsu ya kai kilogiram dubu goma sha huɗu da dari takwas da arba’in da bakwai, 14,847, a yayin samame da bincike da hukumar ke gudanarwa a sassa daban-daban na ƙasar.
Ya ƙara da cewa waɗannan kamen sun taimaka wajen rushe hanyoyin safarar miyagun ƙwayoyi a cikin Nijeriya da ma waje, lamarin da ke nuna cewa ƙasar nan ba za ta lamunci harkar tu’ammali da safarar miyagun ƙwayoyi ba, kamar yadda jaridar Punch ta rawa buba ito.