Jam,iyyar hamayya ta ADC ta soki yadda ake tafiyar da shari’o’in Malami da El-Rufai

Jam’iyyar haɗaka ta ADC ta yi suka kan yadda ake tafiyar da shari’o’in tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai da tsohon ministan shari’a Abubakar Malami tana mai cewa ya kamata a yi amfani da adalci ga kowa ba tare da nuna son rai na siyasa ba.

 

 

 

 

 

A cikin wata sanarwa da sakataren yada labarai na jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya wallafa a shafin X ranar Talata, ya ce ADC na sa ido kan shari’o’in manyan fitattun ƴan siyasarta.

 

 

 

 

 

 

Sanarwar ta jaddada cewa babu ɗan ƙasa da ya wuce doka, amma ta nuna damuwa kan abin da ta kira rashin daidaito a yadda ake aiwatar da matakan shari’a da kuma saurin aiwatar da su a kan El-Rufai da Malami.

 

 

 

 

 

Jam’iyar ta ba da misali da wata shari’a da aka yi a kwanan nan da ya shafi tuhumar laifin ƙirƙirar fasfo ba bisa ka’ida ba da cin hanci da ya shafi ƙasashen waje wanda ta ce har a bayar da belin waɗanda ake tuhuma da laifin a wannan shari’ar.

 

 

 

 

 

 

Amma kuma ba haka ake tafiyar da shari’o’in El-Rufai da Malami ba in ji jam’iyyar.

 

 

 

 

 

Jam’iyyar ta ƙara da cewa, “Abubakar Malami da Nasir El-Rufai ‘yan ƙasa ne kafin su shiga wata jam’iyyar adawa don haka ana ɗaukar su a matsayin waɗanda ba su aikata wani laifi ba a ƙarƙashin Kundin Tsarin Mulki har sai an tabbatar da laifinsu a kotu.”

You might also like
Leave a comment