Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yabawa Shugaban Ƙasa bayan amincewar Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) na sake budawa. tare da haɓaka aikin titin Kano–Kongolom da kuɗinsa ya kai Naira biliyan 334.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, Gwamna Yusuf ya bayyana wannan amincewa a matsayin wani babban ci gaba na tarihi da zai sauya fasalin hanyoyin Kano tare da ƙarfafa matsayin jihar a matsayin cibiyar kasuwanci da sufuri a Arewacin Nijeriya.
Sabon tsarin aikin zai shimfiɗa tazarar kilomita 132, inda za a gina titin mai layi uku (three-lane concrete carriageway), tare da fitilun tituna masu amfani da hasken rana da kuma na’urorin CCTV na zamani domin ƙara tsaro.
Gwamnan ya jaddada cewa titin Kano–Kongolom na haɗa Kano da jihohin Jigawa da Katsina, lamarin da ke sa ya zama muhimmin hanya ta tattalin arziki a yankin Arewa maso Yamma, musamman wajen kasuwanci, noma da bunƙasa masana’antu.
,Ya ce girman jarin da aka zuba a aikin na nuna ƙudirin Shugaba Tinubu na haɓaka Kano da ma yankin Arewa maso Yamma baki ɗaya.
“Aikin zai buɗe sabbin damammaki ga manoma, ‘yan kasuwa da masu sufuri, tare da rage lokacin tafiya da kuma inganta tsaron masu amfani da hanya,” in ji gwamnan.
Haka kuma ya yabawa Ministan Ayyuka, David Umahi, bisa jagorantar ingantattun ayyukan more rayuwa da tabbatar da cewa aikin Kano ya samu fifiko a matakin tarayya.
Gwamna Yusuf ya tabbatar da cewa gwamnatin Kano za ta ba da cikakken haɗin kai da samar da yanayi mai kyau ga ‘yan kwangila domin tabbatar da kammala aikin cikin lokaci.
Ya ƙara da cewa aikin zai samar da ayyukan yi, ya jawo jarin masu zuba jari, tare da ƙara ƙarfafa matsayin Kano a matsayin babbar cibiyar kasuwanci a yankin.
A ƙarshe, gwamnan ya sake jaddada aniyarsa ta ci gaba da hulɗa da Gwamnatin Tarayya kan muhimman ayyukan da za su inganta rayuwar