Majalisar Dokokin Jihar Kano ta fara shirin Tsige Mataimakin Gwamna Aminu Abdussalam Gwarzo Bisa Zargin Rashin Da’a

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta sanya hannu kan wata takardar sanarwa domin fara shirin tsige Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo, bisa zarge-zargen aikata manyan laifuka na rashin da’a, cin zarafin mukami da kuma karya amana.

 

 

 

An gabatar da sanarwar ne a zaman majalisa, inda aka ce an yi hakan ne daidai da Sashe na 188 na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima), wanda ya tanadi yadda ake cire mataimakin gwamna daga mukaminsa.
Yayin gabatar da takardar a gaban majalisa, wani dan majalisa ya bayyana cewa matakin tsige shi ya samo asali ne daga zarge-zarge da suka shafi yadda Abdussalam ya gudanar da aikinsa tun daga lokacin da yake

 

 

 

 

 

Kwamishinan Kananan Hukumomi har zuwa lokacin da ya zama Mataimakin Gwamna.
“Wannan takardar tuhuma wata sanarwa ce ta hukuma daga Majalisar Dokokin Jihar Kano bisa tanadin Sashe na 188 na Kundin Tsarin Mulki kan Aminu Abdussalam,” in ji dan majalisar.

 

 

 

 

 

A cewar takardar, ana zargin mataimakin gwamnan da karbar kudaden alfarma (kickbacks) daga kananan hukumomi 44 na jihar tsakanin watan Yunin 2023 zuwa Janairun 2024.

 

 

 

 

’Yan majalisar sun yi zargin cewa Abdussalam ya rika karbar kimanin Naira miliyan 1.5 duk wata daga kowace karamar hukuma, wanda ya kai kusan Naira miliyan 66 a duk wata, da kuma jimillar Naira miliyan 462 a cikin watanni bakwai.

 

 

 

 

 

Haka kuma, takardar ta ce daga watan Fabrairu zuwa Yulin 2024, ana zargin ya sake karbar karin kudade da suka kai Naira miliyan 726 da sunan gudanar da wasu ayyuka na musamman ga kananan hukumomin.

 

 

 

 

 

Bugu da kari, ’yan majalisar sun zarge shi da amfani da mukaminsa wajen sauƙaƙa fitar da Naira miliyan 440 daga asusun kananan hukumomi 44 zuwa kamfanin Novomed Pharmaceuticals Limited, wanda suka ce ya sabawa dokokin saye da kashe kudaden gwamnati na jihar.

 

 

 

 

 

Majalisar ta bayyana cewa wadannan zarge-zarge gaba daya sun kai matsayin “manyan laifuka na rashin da’a” kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada, kuma ta yanke shawarar a tsige mataimakin gwamnan tare da cire shi daga mukami bisa tanadin doka.

You might also like
Leave a comment