An ceto mutane 166 da aka sace a Kajuru

An ceto ɗaukacin mutane 166 da ƴan bindiga suka yi garkuwa da su daga wasu majam’iu a ƙauyen Kurmin Wali na jihar Kaduna, da ke arewa maso yammacin Najeriya a cewar Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN).

 

 

 

Shugaban ƙungiyar, reshen arewa, Reverend John Hayab ya bayyana cewa duk waɗanda aka sace sun koma gida lafiya, ba tare da biya kuɗin fansa ba.

 

 

 

Shugaban CAN a Kaduna, Reverend Caleb Ma’aji, ya tabbatar da sakin waɗanda aka sace ga BBC.

 

 

 

Ya ce gwamnan jihar ne zai tarbi mutanen a gidan gwamnatin jihar.

 

 

 

Hukumomin gwamnatin Najeriya ba su yi magana kai tsaye game da sakin waɗannan mutane ba.

 

 

 

 

 

 

 

Wannan harin na daga cikin jerin garkuwa da mutane da ke kara matsa lamba kan gwamnatin Najeriya.

 

 

Najeriya ta fuskanci suka daga Shugaban Amurka Donald Trump, wanda ya zargi ƙasar da kasa daƙile abin da ya kira da “kisan Kiristoci.”

 

 

Rundunar Amurka dai ta kai hari kan abin da ta bayyana a matsayin matsugunan ‘yan ta’adda a ranar 25 ga watan Disamba.

 

 

Gwamnati ta ce tana aiki tare da Amurka wajen inganta tsaro

You might also like
Leave a comment