An kashe jami,an ƴan Road Safety fiye da 100 a shekarar 2025 – Shugaban FRSC

Hukumar kiyaye haɗurra ta Najeriya FRSC ta ce an kashe jami’anta fiye da 100 yayin da suke bakin aiki a shekarar 2025 da ta gabata.

 

 

 

Hukumar ta bayyana cewa ƙaruwar  yawan mutuwar jami’anta ya sa ta fara kira ga gwamnatin tarayya da ta ba ta damar bai wa jami’anta makamai domin kare kansu, tare da ƙara musu kwarin gwiwa yayin gudanar da aikinsu a kan hanyoyi.

 

 

 

Shugaban hukumar FRSC, Shehu Mohammed ya shaida wa BBC cewa direbobi ne yawanci suke buge jami’an yayin da suka kan bakin aikinsu.

 

 

 

“A shekarar da ta wuce mun shiga juyayi na rasa kusan jami’anmu 127, kuma kusan dukkansu direbobi ne suka buge su suna kan aiki lamarin da ke ci maana tuwo a ƙwarya,” in ji shi.

 

 

 

Ya ce abin da ya fi tayar musu da hankali shi ne yadda wasu direbobi ke buge jami’ansu ɗin duk da cewa suna tsaye ne a gefen hanya.

 

 

 

“Abin takaici shi ne wani direba zai buge jami’anmu alhali suna kan gefen hanya. Wasu lokutan ma kamar da gangan ake yi. Wannan ne ya sa kullum muke ƙara faɗakar da direbobi su guji shan giya ko wani abu mai sa maye kafin su zauna kan tuƙi,” in ji shugaban hukumar.

 

 

 

 

Shugaban hukumar ya ƙara da cewa bai wa jami’an FRSC damar riƙe makami zai zama wata hanya ta rage irin waɗannan haɗurra.

 

 

 

“Shi ya sa muke ta kira da a bar jami’anmu su riƙe makami. Wannan zai bayar da kwarjini, zai ƙara musu ƙarfin gwiwa, kuma direbobi za su ji tsoron yin wani abu da zai cutar da su,” in ji shugaban.

 

 

 

Sai dai ya jaddada cewa idan aka amince da batun riƙe makami, horo mai tsauri shi ne abu mafi muhimmanci dsa za su fifita.

 

 

 

“Idan aka ba mu dama mu riƙe makami, horo ne zai zama na farko. Horo ne zai kawo hankali, zai sa a bi doka, kuma zai sa jami’i ya fahimci haƙƙin ɗan Adam, ta yadda ba zai yi amfani da makami wajen cutar da wani ba,” in ji shi.

You might also like
Leave a comment