Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) na tuhumar tsohon gwamnan kogi yahaya Bello da laifuka guda 19 da suka shafi almundahanar kuɗi har kimanin ₦80,246,470,088.88.

A  ranar Laraba, 4 ga Fabrairu, 2026,  Mai Shari’a Emeka Nwite na Babbar Kotun Tarayya da ke Maitama, Abuja, inda aka yi wa Shaida ta Bakwai (PW7) tambayoyi a ƙarƙashin rantsuwa.

 

 

A zaman kotun, lauyan masu gabatar da ƙara, Kemi Pinheiro, SAN, ya bayyana cewa an ware ranar ne domin ci gaba da yi wa PW7 tambayoyi, yana mai ƙarawa  da cewa suna da shaidu uku a shirye.

 

 

Olomotane Egoro, jami’in kula da bin ƙa’idoji na  Access Bank Plc, ya tabbatar da cewa yana ƙarƙashin rantsuwa. Yayin tambayoyin da lauyan ɓangaren kariya, J.B. Daudu, SAN, ya yi masa,

 

 

shaida ya ce ya bayar da shaidarsa ne bisa sammaci (subpoena), kuma ya gabatar da hujjoji da aka yi wa alama da Exhibits 32, 33 (1–11), da 34. Ya kuma amince cewa ya taɓa bayar da shaida a wata Babbar Kotun Tarayya kan waɗannan hujjojin, sai dai bai tuna sunayen waɗanda ake tuhuma ba ko kuma  shi ne PW2 a wancan shari’ar.

 

 

 

Yayin da ɓangaren kariya ke ƙoƙarin gabatar da Kwafin Takardun da aka Tantance (Certified True Copies – CTCs) daga waccan kotu,

 

 

lauyan masu ƙara ya ce ba su da adawa da takardun, amma ya nuna akwai matsala ta bin ƙa’ida saboda ba a gabatar da rasitin biyan kuɗin fitar da CTCs ba. Ya kuma jaddada cewa shaidar ta kasance mai daidaito a jawabansa.

 

 

Mai Shari’a Nwite ya amince da hujjar masu ƙara, inda ya ce sai an gabatar da rasitin biyan kuɗin kafin a karɓi takardun. Daga nan, ɓangaren kariya ya sanar da kotu cewa suna ƙoƙarin samo rasitocin.

 

 

Tambayoyin sun kuma mayar da hankali kan mu’amalar kuɗi da ta shafi Keyless Nature Limited, Fazab Oil, da Abba Adaudu. Shaidar ya tabbatar da biyan kuɗi ta counter cheque a reshen Access Bank na Otukpo, da kuma wasu canje-canje da suka haɗa da ₦200,000 da ₦8 miliyan da aka tura wa Abba Adaudu.
Game da kuɗaɗen da suka shigo daga ƙananan hukumomi, shaida ya ce an biya kuɗaɗe ne don takamaiman ayyuka, ciki har da:

 

₦7,500,144.61 daga Ƙaramar Hukumar Okehi domin sayen kayan asibiti;
₦10,863,247.50 daga Ƙaramar Hukumar Omala a ranar 3 ga Yuni, 2022, domin sayen kayan wasanni;
₦12,228,400.10 daga Ƙaramar Hukumar Yagba East a ranar 6 ga Yuni, 2022, domin sayen kayan kiwon lafiya.

 

 

 

 

Ya kuma bayyana cewa bayanan da ke cikin Exhibit 33(11) sun yi daidai da mu’amalolin banki na yau da kullum, sannan takardun buɗe asusun Fazab Oil ba su nan take, amma za a iya samo su.

 

 

 

 

Daga bisani, Mai Shari’a Nwite ya ɗage shari’ar zuwa ranar Alhamis, 5 ga Fabrairu, 2026, domin ci gaba da yi wa PW7 tambayoyi.

You might also like
Leave a comment