Majalisar dunkin duniya ta ware dukkannin 4 ga fabareru ranar wayar da kan mutane akan cinwo daji (cancer)

A dukkannin ranar 4 ga watan Fabarairun kowacce shekara Majalisar dinkin Duniya ke warewa a matsayin ranar wayar da kan jama’a dangane da Ciwon Daji (Cancer).

 

 

 

 

A don haka ne ma kungiyar Masana kuma Kwararru a fannin Cimakar Abinci ta kasa reshen jihar kano Karkashin jagorancin Shugaban Kungiyar Dr Auwal Musa Umar suka yi tattaki daga Asibitin yara dake kan titin zuwa Gidan Zoo, zuwa Asibitin Koyarwa na Malam Aminu kano.

 

 

A yayin zantawar sa da manema labarai, Auwal yace, sun fito ne domin wayar da kan jama’a da kuma fadakar dasu akan illar Cutar daji da kuma Abincin da ya kamata mutane su guje masa da rungumar wasu Abinci musamman na Gargajiya

 

 

 

A karshe yayi kira ga Al’umma dasu kasance masu mika rahoton bullar sabuwar cuta da aka kasa gane ta a Jikin mutum zuwa Asibiti mafi kusa domin daukar Matakin Gaggawa.

You might also like
Leave a comment