Yan bindiga sun kai hari kwara inda Ake fargabar waɗanda ƴan bindiga suka kashe sun kai 70

Jami’an agajin gaggawa na Red Cross a Najeriya sun ce ana fargabar adadin mutanen da ƴan bindiga suka kashe a jihar Kwara ya kai kusan 70, biyo bayan wani mummunan hari da aka kai a ƙauyen Woro.

 

 

 

Red Cross ta ce har yanzu akwai mutanen da ba a gano inda suke ba tun bayan harin, inda ƴan bindigar suka kuma banka wa shaguna wuta tare da ƙone gidan sarkin gargajiya na yankin.

 

 

 

A wani lamari na daban, rahotanni daga jihar Katsina da ke arewacin ƙasar na nuna cewa aƙalla mutum 21 daga cikin mazauna ƙauyuka ne suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren ƴan bindiga.

 

 

 

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta ƙara ƙaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma, a daidai lokacin da hare-haren kan fararen hula ke ƙaruwa a sassan arewa da tsakiyar ƙasar.

 

 

 

Hukumomi da jami’an tsaro sun ce ana ci gaba da bincike da kuma ƙoƙarin gano mutanen da suka ɓace, yayin da al’umma ke fatan ɗaukar matakai masu inganci domin daƙile yawaitar hare-haren ƴan bindiga.

 

You might also like
Leave a comment