Nuhu Ribadu ya ƙaddamar da shirin taimakawa matasa domin yaƙi da ta’addanci da fashi da makami a fadin nigeria
Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da wani sabon shiri na taimakawa matasa da nufin magance matsalolin tsaro kamar fashi da makami, ta’addanci da sauran ayyukan laifi a faɗin ƙasar nan.
An ƙaddamar da shirin mai suna (Safe Nigeria Initiative), wanda kuma ake kira Youth Empowerment for Peace and Resilience, a ranar Talata a Abuja.
Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro (NSA), Nuhu Ribadu ne ya ƙaddamar da shi, ta hannun Babban Kwamandan Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci ta Ƙasa (NCTC), Manjo Janar Adamu Laka.
Shirin na ƙarƙashin jagorancin Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci (NCTC) tare da haɗin gwiwar Ofishin Babbar Mataimakiya ta Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Harkokin Jin-ƙai da Rage Talauci.
A jawabinsa, Ribadu ya ce an tsara shirin ne domin ya taimaka wa ƙoƙarin da ake yi na yaƙi da matsalolin tsaro ta hanyar magance tushen matsalolin. Ya ce talauci, rashin aikin yi, wariya da kuma raɗaɗin rikice-rikice na daga cikin abubuwan da ke janyo matasa shiga ta’addanci, fashi da makami da garkuwa da mutane.
Ya jaddada cewa matakan da suka shafi jama’a kai tsaye, ba amfani da ƙarfi kawai ba, su ne mabuɗin samar da zaman lafiya mai ɗorewa.
Shirin zai tallafa wa matasa marasa galihu ta hanyar ba su horo kan sana’o’i, tallafin dogaro da kai, kula da lafiyar kwakwalwa da kuma ilimin zaman lafiya da ƙasa, domin rage yiwuwar jawo su shiga ƙungiyoyin ta’addanci da laifi.
An bayyana cewa za a aiwatar da shirin a duk faɗin ƙasar nan, inda ake sa ran sama da matasa 11,000 za su amfana da shi.
Ita ma Babbar Mataimakiya ta Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Harkokin Jin-ƙai da Rage Talauci, Misis Delu Yakubu, ta ce shirin ya yi daidai da ajandar Renewed Hope ta Shugaba Bola Tinubu, wadda ta fi mayar da hankali kan inganta rayuwar jama’a da samar da damammaki.
Ministan Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Sanata Atiku Bagudu, ya ce yawan matasan Najeriya wata babbar dama ce ga ci gaban ƙasa, yana mai cewa zuba jari a horar da su zai taimaka wajen rage rashin aikin yi da matsalolin tsaro.
Shi kuma Darakta Janar na Ƙungiyar Gwamnonin Jihohi, Abdulateef Shittu, ya ce ba za a iya samun cikakken tsaro ta hanyar amfani da ƙarfi kaɗai ba, yana mai tabbatar da cewa gwamnatocin jihohi za su ba da goyon baya wajen aiwatar da shirin ta hanyar haɗin gwiwa da al’umma.
An ƙaddamar da wannan shiri ne a daidai lokacin da ƙasar ke fuskantar ƙalubalen tsaro, inda ake danganta yawancin matsalolin da rashin aikin yi, talauci da kuma wariyar zamantakewa tsakanin matasa.