DSS ta gurfanar da Malami da ɗansa kan zargin mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba.
Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta gurfanar da tsohon Babban Lauyan Tarayya (AGF) kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, tare da ɗansa Abdulaziz a gaban Kotun Tarayya da ke Abuja kan tuhume-tuhume guda biyar da suka shafi zargin ta’addanci da mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba.
A cikin takardar ƙarar da aka shigar a kotu, an zargi Malami da sanin wasu masu tallafa wa ta’addanci amma ya ƙi gurfanar da su a lokacin da yake riƙe da muƙamin AGF da Ministan Shari’a.
Haka kuma, an zarge shi da ɗansa da ajiye makamai a gidansu da ke Gesse Phase II a Birnin Kebbi, Jihar Kebbi, ba tare da lasisi ba.
A ƙididdiga ta farko, DSS ta ce Malami ya taimaka wa masu tallafa wa ta’addanci ta hanyar ƙin gurfanar da su, duk da cewa an kai masa bayanan shari’arsu a ma’aikatar shari’a.
A ƙididdiga ta biyu zuwa ta biyar, Malami da ɗansa ana zarginsu da:
Mallakar bindiga kirar Sturm Magnum 17-0101 ba tare da lasisi ba,
Mallakar harsasai guda 16 na Redstar AAA 5’20,
Da kuma harsasai 27 da aka riga aka harba (expended cartridges),
wanda ake zargin sun aikata sabanin dokokin Terrorism (Prevention and Prohibition) Act, 2022 da kuma Firearms Act, 2004.
Martanin kotu
Dukkaninsu sun musanta laifukan lokacin da aka karanta musu tuhume-tuhumen a kotu.
Bayan haka, lauyan gwamnati, Calistus Eze, ya roƙi kotu ta tsare su a hannun DSS tare da sanya ranar fara shari’a.
Sai dai lauyan masu kare kansu, Shuaibu Aruwan (SAN), ya nemi a ba su beli, yana mai cewa sun shafe sama da makonni biyu a tsare.
Mai shari’a Joyce Abdulmalik ta ƙi amincewa da neman belin ta baki, tana mai cewa dole ne a shigar da cikakken buƙata a rubuce, sannan ta umarci a ci gaba da tsare su a hannun DSS.
An ɗage shari’ar zuwa ranar 20 ga Fabrairu domin fara sauraron ƙarar.
Shari’ar na ɗaukar hankalin jama’a duba da cewa Malami ya taɓa rike muƙamin Babban Lauyan Tarayya a baya.