Kungiyar darikar Kwankwasiyya ta musanta iƙirarin saka sharaɗi don sauya sheƙar Kwankwaso zuwa jam,iyyar APC
Ƙungiyar Kwankwasiyya ta musanta ikirarin da wasu ke yaɗawa na cewa jagaran tafitar Dokta Rabi’u Musa Kwankwanso ya saka sharaɗin komawarsa APC.
Wasu rahotonni da ke yawo musamman a shafukan sada zumunta sun yin iƙirarin cewa jagoran Kwankwasiyyar na tattaunawa da jiga-jigan APC tare da saka sharaɗin komawarsa jam’iyyar.
Cikin wata sanarwa da ta fitar, Kwakwasiyya ta bayyana matuƙar damuwa kan yawaitar rahotanni ikirarin ficewar Dokta Kwankwanso daga jam’iyyarsa ta NNPP zuwa jam’iyyar APC.
Ƙungiyar ta bayyana waɗannan rahotanni a matsayin tsagwaran ƙarya marasa tushe kuma an ƙirƙiresu ne domin ruɗar da al’umma.
“Sanata Kwankwaso bai taɓa shiga wata tattaunawa ko ganawa ko shawarwari da jam’iyyar APC ko Shugaba Bola Ahmed Tinubu ko wakilansa ba kan batun sauya sheƙa,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta ci gaba da cewa “babu wata hujja da ke goyon bayan waɗannan zarge-zarge da ake yaɗawa.”
Ƙungiyar ta kuma caccaki wasu kafafen watsa labarai da masu sharhi kan siyasa, tana mai cewa “abin takaici ne a riƙa wallafa zarge-zarge masu girma ba tare da bincike mai zurfi ba ko tabbatarwa daga wanda abin ya shafa ba.”
Kwankwasiyya ta bayyana cewa “ganawar da aka taɓa yi tsakanin Kwankwaso da Shugaba Tinubu ta ƙarshe ta faru ne a watan Janairun 2024, kuma babu wata magana da aka yi a lokacin kan ficewa daga jam’iyya ko wata yarjejeniyar siyasa.”
Ta ƙara da cewa hulɗar Kwankwaso da shugabanni daga jam’iyyu daban-daban abu ne na al’ada a tsarin dimokuraɗiyya, kuma bai kamata a juya hakan zuwa labaran bogi ba.
Ƙungiyar ta kuma bayyana cewa tana ganin waɗannan rahotanni wani yunƙuri ne na ɓata sunan Kwankwaso da rage tasirinsa a siyasar ƙasa inda ta baƙacin ƴan Najeriya su yi watsi da rahotannin ƙarya.