Neco tasaki sakamakon jarabawar SSCE ta shekarar 2025

Hukumar Shirya Jarabawa ta Ƙasa (NECO) ta sanar da fitar da sakamakon jarabawar Babbar Sakandare ta  (SSCE) ta shekarar 2025.

 

 

Da yake jawabi a hedikwatar hukumar da ke Minna, Jihar Neja, Rajistara  NECO, Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi, ya ce an rubuta darussa 16 a jarabawar, kuma jimillar dalibai 96,979 ne suka yi rajista.

 

 

 

Daga cikin adadin, maza sun kai 51,823, wato kashi 53.43 cikin 100, yayin da mata suka kai 45,156, wato kashi 46.56 cikin 100.

 

 

Ya kara da cewa dalibai 95,160 ne suka zauna jarabawar. A darasin Turanci kuwa, dalibai 93,425 ne suka rubuta, inda 73,167 daga cikinsu, wato kashi 78.32 cikin 100, suka samu makin credit da sama.

 

 

 

Haka kuma a darasin Lissafi, dalibai 93,330 ne suka rubuta, kuma 85,256 daga cikinsu, wato kashi 91.35 cikin 100, suka samu credit da sama.

 

 

A cewarsa, dalibai 68,166, wato kashi 71.63 cikin 100, sun samu darussa biyar da credit da sama ciki har da Turanci da Lissafi.

 

 

 

Sannan dalibai 82,082, wato kashi 86.26 cikin 100, sun samu darussa biyar da credit da sama ba tare da la’akari da Turanci da Lissafi ba.

 

 

Sai dai Farfesa Wushishi ya bayyana cewa an kama dalibai 9,016 da laifuffukan satar jarabawa, wanda hakan ya nuna karin kashi 31.7 cikin 100 idan aka kwatanta da dalibai 6,160 da aka kama a shekarar 2024.

 

 

 

Ya kuma sanar da cewa an ba da shawarar sanya ido na dindindin  ga masu kula da jarabawa guda biyar—biyu daga Babban Birnin Tarayya (FCT), sai daya daga Kano, daya daga Adamawa da daya daga Ondo—saboda taimakawa wajen aikata magudin jarabawa.

 

 

 

Bugu da kari, an ba da shawarar cire amincewa (de-recognition) ga cibiyoyi hudu—biyu daga Jihar Neja, sai daya daga Yobe da daya daga Kano—saboda samunsu da hannu a magudin jarabawa na gaba daya a cibiyar.

You might also like
Leave a comment