An Kama Wasu Ma’aurata da suka kitsa Garkuwa Da Kansu, Tare Da Karɓar Miliyan 10 Matsayin Kudin Fansa
An kama wasu ma’aurata mazauna jihar Legas bisa zargin su da kitsa garkuwa da kansu tare da karɓar Naira miliyan 10 daga dangi da abokansu a matsayin kudin fansa.
Aminiya ta gano cewa ma’auratan, masu suna Fred da Goodness, sun ƙirƙiri labarin sacewar a ranar 7 ga watan Janairu domin neman kuɗi ga mijin, wanda ya yi niyyar komawa Amurka saboda rashin tallafin kuɗi.
Wani jami’in ’yan sanda da ya yi magana da Jaridar a ranar Alhamis ya ce ma’auratan sun tuntubi ’yan uwa daga danginsu, suna ikirarin cewa an sace su tare da neman kudin fansa.
Dangin sun tattara Naira miliyan 10 cikin kwana uku, suna zaton kuɗin zai taimaka wajen kubutar da su.
Jami’in ya ce ma’auratan sun tsara wurin karɓar kuɗin a wata makaranta da ke Cappa, Mushin.
“Jami’an da ke sa ido sun lura da matar ta shiga wurin ita kaɗai, daga baya mijin ya iso. Amma an fara zargin su bayan sun fito tare da jakar kuɗi. An bincika jakar, aka gano kudin fansa, nan take aka kama su,” in ji shi.
Matar ta bayyana cewa ita ce ta shawarci mijinta su kitsa wannan shiri.