Dalilin da ya sa gwamnonin APC ba su damu da barazanar tsige Fubara ba_Abdullahi sule

Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya ce gwamnonin da aka zaɓa a ƙarƙashin jam’iyyar APC ba su damu sosai da yunƙurin tsige Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara ba, domin batun yana gaban kotu.

 

 

Sule ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin da yake magana a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels.

 

 

 

Da aka tambaye shi ko gwamnonin APC na cikin damuwa kan yiwuwar tsige ɗaya daga cikinsu, da kuma ko suna shirin shiga tsakani, Sule ya ce tsarin tsige gwamna yana tafiya ne bisa doka da ka’ida.

 

 

 

Ya ce, “Ba na cikin damuwa saboda batun yana gaban kotu. Ba za ka iya tashi kawai ka tsige gwamna ba tare da bin ƙa’ida da tsarin doka ba.”

 

 

Ya ƙara da cewa duk da cewa duk abin da ya shafi wani gwamna yana damun su a matsayinsu na abokan aiki, ba su kai ga yanke hukuncin cewa lallai za a tsige Fubara ba.

 

 

 

“A zahiri duk abin da ya faru da ɗaya daga cikinmu abin damuwa ne, amma ba mu kai ga matakin da za mu ce dole sai an tsige shi ba,” in ji Sule.

 

 

Ya kuma bayyana cewa matakan shari’a da na kundin tsarin mulki suna gudana domin warware batun.

 

“A halin yanzu, kotuna suna yanke hukunci, sannan Alkalin Alkalai ya riga ya ɗauki matsayi. Saboda haka ba mu da wani dalilin damuwa,” in ji shi.

 

 

A gefe guda kuma, sabon yunƙurin tsige Gwamna Fubara ya tsaya cak sakamakon ƙalubalen shari’a da na tsarin doka.

 

A ranar 23 ga Janairu, 2026, Babbar Kotun Jihar Rivers da ke zamanta a Oyigbo ta ɗage sauraron ƙarar tsige gwamnan har sai baba-ta-gani, tana mai cewa dole ne Kotun Ɗaukaka Ƙara ta fara yanke hukunci kan ƙorafe-ƙorafen da Kakakin Majalisa da wasu ‘yan majalisa suka shigar. Wannan hukunci ya dakatar da duk wani mataki na ci gaba da tsige shi.

 

 

Haka kuma, Alkalin Alkalai na Jihar Rivers, Mai Shari’a Simeon Amadi, ya ƙi kafa kwamitin bincike kan batun, yana mai cewa akwai umarnin kotu da ke aiki, kuma bai dace kotu ta saurari batu da ke gaban wata kotu ba.

 

 

Wannan shi ne yunƙuri na uku na tsige Gwamna Fubara cikin ƙasa da shekaru uku.

 

 

‘Yan majalisar sun zarge shi da manyan laifuka, ciki har da gaza gabatar da kasafin kuɗi, zargin kashe kuɗaɗen jama’a ba tare da izini ba, riƙe kuɗaɗen majalisa, da kuma rushe ginin majalisar dokoki a shekarar 2023.

You might also like
Leave a comment