Babbar Kotun magistire mai lamba 34 a unguwar koki ta aike da Ibrahim sunday gidan kaso
Daga Babbar kotun Majistare Mai lamba 34 dake zaman ta a Unguwar Koki Karkashin jagorancin mai shari’ah Farouk Ibrahim Umar.
An Gurfanar da Ibrahim Sodey me kimanin shekaru 55 mazaunin Unguwar Rijiyar Zaki bisa zargin hada kai da aikata fashi da makami ga wani mutum me suna Alhaji Muhammad Kabir dake zaune a Unguwar titin zuwa Filin tashi da Saukar Jiragen Sama na Malam Aminu kano.
Wanda suka Farmake shi da muggan makamai da suka hadar da Bindiga, Adda da sauran makamai Masu Hadari.
Wanda hakan ya sanya shi Cikin Firgici da tsoro, Nan take suka kwace masa Wayoyin hannu, Katin Shaida wato I.D CARD, da Hula da Kuma Takalma da kawo yanzu ba’a San kimar kudin su ba.
Bayan da Lauyar Gwamnati Barr Zainab Danjuma ta karanto kunshin tuhumar da ake masa nan take ya musanta, inda me shari’ah ya bayar da Umarnin a ajiye shi a Gidan ajiya da Gyaran hali zuwa ranar 23 ga watan Fabarairun da muke Ciki domin Cigaba da sauraron karar.
Tunda farko dai, Alhaji Kabiru ne ya dauki Ibrahim Sodey a matsayin Wanda suke yin aiki tare, amma daga bisani Ibrahim yaci Amanar sa ta yi masa Barazana har aka Gurfanar da Ibrahim Sodey gaban kotun Majistare Alkali Mansur.