Wata baiwar Allah ta koka game da kasancewarta tafito daga babbar zuria anan kano amma hakan bai amfanar da ita komaiba
A yammacin ranar asabar din data gabata ne kafar yada labarai ta GTRHAUSA ta zanta da hafsat hashim usman Mai lalurar kugu wadda ke neman taimako
hafsat ta bayyana GTRHAUSA cewar ta gamu da lalurar kugo wadda yake neman zama silar rasa kafar ta
A irin kokarin da sukai a matakin farko anyi Mata aiki a asibitin murtala inda ba a samu dace ba bayan Nan aka tura su asibitin Kashi na dala wato orthopedic hospital inda ka rubuta abinda za a kashe Wanda ya tasar ma miliyan shid 6,000,000
Yan uwa makusantantan hafsa sun nemi taimakon “Yan uwa na kusa Dana nesa Amma abin ya gagara duk da ta hada jini da gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir yusif da Kuma sarkin Kano malam Muhammad sunusi na ll
mun tura takarda ga gwamnatin jihar Kano Amma abin yaki ci yaki cinyewa mun tura ga jagororin zuri’ar gwani mamman zahraddin Amma abin Shiru Kamar maye yaci shirwa
wannan lalura tana Hana ni bacci ciwan yau daban na gobe daban
hafsa hashim usman