Akalla gidaje biyu aka kone a karamar hukumar igabi ta jahar kaduna sakamakon rikicin matasa kan hakar ma,adanai
Aƙalla gidaje biyu ne aka ƙona tare kuma da jikkata shugabannin al’umma bayan wani rikici tsakanin matasa a karamar hukumar Igabi na jihar Kaduna.
Rikicin wanda ya ɓarke a ranar Lahadi zuwa safiyar litinin , ya faru ne sakamakon saɓani kan ayyukan haƙar ma’adinai, kamar yadda mazauna yankin suka shaida wa jaridar Daily Trust.
Wani shugaban al’umma, Malam Ahmad Mishigi, ya ce rikicin ya shafi matasan anguwar Mishigi da kuma na anguwar Kudu ne kan batun haƙar ma’adinai.
“Maganar gaskiya ita ce, rikici ne tsakanin matasa. Ya fara ne sakamakon saɓani kan samun abin saka wa a bakin salati,” in ji Malam Ahmad.
Ya ce saɓanin wanda ya fara a shekarar da ta gabata, ya rikiɗe zuwa tashin hankali tsakanin makwabta, inda lamarin ya munana a ranar Lahadi.
Ya ce duk irin koƙari da shugabanni suka yi na kwantar da tarzomar abin ya citura, inda aka jikkata wasu daga ciki.
Sai dai, kakakin ƴansandan jihar ta Kaduna, DSP Mansir Hassan, ya ce tuni aka shawo kan lamarin.