yan mata da matan aure da zawarawa sun amfana da koyon sana,oi domin dogoro da kai daga kungiyar muryar matan arewa.

← Back

Thank you for your response. ✨

kungiyar muryar matan arewa tayi bikin yayi dalibai 55 a a ranar asabar 31-1-2026  an gudanar da taron a gidan magajin garin kano dake yakasai

 

 

 

taron ya samu halartar shuwagabanni na siyasa da jagororin Al’umma hadi da iyayan yaran da aka Yaya “ya”Yan nasu

 

 

 

a nata jawabin shugabar kungiyar muryar matan arewa hajiya binta muhammad shata ta godewa Allah bisa wannan nasara da suka samu ta kara da cewa wannan ba shine Karin farko da kungiyar ta fara wannan kin ba ta dauki tsawan lokaci

 

 

 

sana’o’in da matan suka koya sun hadar da man shafawa dinki bonvita madara kayan lashe lashe da tande tande yin mayafai hada lemuka da sauran su

 

 

 

a nasa jawabin dan goriban Kano Alhaji Abubakar sule gaya ya yabawa wadannan Mata tare da Kira ga gwamnan jihar Kano daya ribanya aikin da yake akan na yanzu musamman akan matasa.

 

 

 

mai girma magajin garin kano Alhaji nasiru wada Wanda Alhaji junaidu ya wakilta ya bayyana farin cikin sa na yadda ake kokari wajan Gina rayuwar matasa

 

 

 

naja’atu Muhammad Abdullahi dake a matsayin shugabar shirye shirye na kungiyar muryar matan arewa ta godewa Allah hadi da Kira g masu hali dasu ninka kokarin da suke akan Wanda sukeyi musamman ma marayu na nesa Dana kusa

 

 

 

a nasu bangaran daliban sun bayyana godiyar su da jin dadin su

 

 

a karshe ya raba shaidar kammala horan ga dalibai hamsin da biyar

You might also like
Leave a comment