Shugaban kungiyar matsakaitan yankasuwar kwanar singa Alh sammani gama mai nasibi ya bayyana cewa kungiyarsu tana tare shugaban darikar kwankwasiya sanata rabiu kwankwaso

Shugaban kungiyar matsakaitan yankasuwar kwanar singa Alh sammani gama mai nasibi ya bayyana cewar, har yanzu suna tare da Shugaban kungiyar Darikar Kwankwasiyya na Duniya Dr Rabiu Musa kwankwaso a cikin jamiyyar NNPP duk da cewar wasu mutanen sun fice daga cikin jamiyyar.

 

 

 

Alh Sammani gama ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a nan jihar Kano.

 

 

 

Sammani gama mai nasibi ya ce, ficewar wasu mutane ba zai basu tsaro wajen gujewa Dr. Rabiu Musa kwankwaso ba, sai ma kwarin gwiwa da suka karawa sauran alummar da suka rage a cikin jamiyyar ta NNPP.

 

 

 

Matashin Dankasuwar yayi kira ga ‘ya’yan jamiyyar NNPP da su kwantar da hankulansu wajen hada kansu guri guda tare da tunkarar matsalolin da za su Kara kawo daidaito a tsakanin junansu,maimakon tunanin wane da wane sun fice daga cikin jamiyyar.

 

 

 

Yace akwai managartan tsare tsare da jamiyyar NNPP take kokarin tankadar domin Samar da da kyakyawan shugabancin da zai ciyar da alummar jihar Kano gaba, musamman a wannan lokacin da jama’ar jihar Kano da na kasa suke Neman mafita.

 

 

 

Daga karshe yana hakurtar da alummar Kano dangane da abin daya faru tsakanin injiniya Abba Kabir Yusuf da madugun Darikar Kwankwasiyya na Duniya Dr Rabiu Musa kwankwaso.

You might also like
Leave a comment