Sojojin Najeriya sunyi nasarar kashe wani kwamandan Boko haram a dajin Sambisa
Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Operation Hadin Kai da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya, sun yi nasarar kashe wani babban jigo na ƙungiyar Boko Haram/ISWAP mai suna Abu Khalid.
An kashe Khalid wanda shi ne babban kwamandan Boko Haram na biyu a dajin Sambisa, tare da wasu mayaƙansa 10 a wani samame da suka kai cikin dare a jihar Borno.
Jami’in yaɗa labarai na rundunar, Laftanar-Kanar Sani Uba ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.
“Sa’o’i 24 bayan sojoji sun kawar da gawurtacen kwamandan Boko Haram/ISWAP, Julaibib, wanda ke aiki a yankin Gujba, dakarun haɗin gwiwa sun yi artabu da mayaƙa a yankin ƙaramar hukumar Komala da ke Konduga da misalin ƙarfe 11 na dare.” in ji sanarwar
A cewarsa, sojojin sun samu nasarar kwace bindigogi ƙirar AK-47 guda biyar, da alburusai, da kekuna da dama, da kayan aiki iri-iri da kayan abinci, da kuma magunguna masu tarin yawa.
Uba ya ce ba a rasa ko soja ɗaya ba a yayin samamen, kuma rundunar tana ci gaba da gudanar da aikin fatattakar mayaƙan Boko Haram/ISWAP da ke addabar yankin.