Kungiyar mutuka motocin haya rashen jahar kano sunroki gwamnati tawo musu dauki

Kungiyar manuka motocin haya ta kasa reshen jihar Kano tana ci gaba da yin kiraye kirayen Gwamnatin ta kawo musu dauki gaggawa saboda yadda tashar ta yi musu kadan .

 

 

 

Mataimakin shugaban kungiyar Alh Samaila sale greedy ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a nan jihar Kano.

 

 

 

Shugaban kungiyar yace yanzu haka Tashar tayi musu kadan a don haka suke ta yin kira ga Gwamnatin tayi duk maiyiyuwa domin fitar da ‘ya’yan kungiyar daga cikin halin matsin rayuwar da suka samu kansu a ciki.

 

 

 

Idon ba’a manta ba, kungiyar tashar Mal. Kato ta baiwa Gwamnatoci da dama hadin Kai yadda ya kamata,amma yanzu lamarin Bata sauya zani ba.

 

 

 

Kungiyar ta bukaci Wadanda suke da ruwa da tsaki akan tashar Malam kato, da su kawo mata daukin gaggawa duba da alummar da suke cin abinci acikinta.

You might also like
Leave a comment