Bello turji yana tsaka mai wuya -commandan rundunar hadin gwiwar operations fansar yamma
Kwamandan Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma wato Operation Fansan Yamma, Manjo Janar Warrah Idris, ya bayyana cewa ƙasurgumin ɗan bindiga Bello Turji na cikin matsanancin firgici da rudani sakamakon tsananta hare-haren da sojojin Nijeriya ke kai masa a wuraren buya.
Manjo Janar Warrah Idris ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da yake zantawa da ’yan jarida a wani rangadi da suka kai jihar Zamfara, inda ya ce matsin lambar da dakarun soji ke yi ya tilasta wa Bello Turji yawan sauya maɓoyarsa domin neman tsira.
Ya ƙara da cewa hare-haren da Rundunar Operation Fansan Yamma ke kaiwa sun takura Bello Turji da sauran shugabannin ’yan bindiga a yankin Arewa maso Yamma, lamarin da ke nuna cewa sojojin Nijeriya na ci gaba da samun nasarori wajen fatattakar ayyukan ta’addanci a yankin.